Dakatar da Sanata Ningi: Tinubu Ya Sanya Labule da Shugabannin Majalisa, Bayanai Sun Fito
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga wata ganawa ta sirri da shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, a fadar Aso Rock Villa
- Ganawar ta haɗa da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin da wasu sanatoci na zuwa ne bayan majalisar ta dakatar da Abdul Ningi
- Majalisar dattawan dai ta dakatar da sanata mai wakiltar Bauchi ta tsakiya bayan ya yi zargin cewa an yi cushen N3.7tr a cikin kasafin kudin 2024
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya shiga ganawar sirri da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, da wasu sanatoci a fadar Aso Rock Villa, Abuja.
Tattaunawar ta ranar Talata ta biyo bayan dakatarwar da majalisar ta yi wa Sanata Abdul Ningi mai wakiltar Bauchi ta tsakiya a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP, cewar rahoton jaridar The Punch.
Jaridar Vanguard ta ce shugaban majalisar dattawan bai yi magana da ƴan jarida ba bayan sun kammala ganawa da shugaba Tinubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ningi ya yi zargin yin cushe a kasafin kuɗi
Sanata Abdul Ningi dai ya zargi gwamnatin tarayya da aiwatar da wani kasafin kuɗi saɓanin wanda majalisar dattawa ta amince da shi a ranar 1 ga watan Janairu, 2024.
Ningi, wanda shi ne shugaban ƙungiyar Sanatocin Arewa da kuma kwamitin majalisar dattawa mai kula da yawan jama’a, ya bayyana hakan ne a wata hira da sashen Hausa na BBC.
A cewar sanatan, majalisar dattawa ta amince da kasafin kuɗi ne na N25tn, ba kasafin kuɗi na N28.7tn da ake aiwatarwa a halin yanzu ba.
A ranar Litinin, Ningi ya sake jaddada iƙirarinsa na cewa N3.7tn ba a san inda ta yi ba a cikin kasafin kuɗin na 2024.
A zaman da majalisar ta yi a ranar Talata, 12 ga watan Maris 2024, ta dakatar da Ningi na tsawon watanni uku saboda zargin da ya yi na yin cushe a cikin kasafin kuɗin.
An hautsine a majalisa
A wani labarin kuma, kun ji cewa an hautsine a majalisar dattawa yayin da ake muhawara kan zargin da Sanata Abdul Ningi ya yi na cushen N3.7tr a kasafin kuɗim shekarar 2024.
A yayin mahawarar wata sabuwar dambarwa ta ɓarke a majalisar kan zargin fifita wasu sanatoci wurin rabon kuɗaɗe.
Asali: Legit.ng