Shugaba Tinubu Ya Fayyace Gaskiya Kan Masu Zargin Buhari Ne Ya Lalata Najeriya

Shugaba Tinubu Ya Fayyace Gaskiya Kan Masu Zargin Buhari Ne Ya Lalata Najeriya

  • Bola Ahmed Tinubu ya nesanta kansa daga cikin muƙarraban gwamnatinsa da ke zargin Muhammadu Buhari, da jefa Najeriya cikin kakanikayi a mulkinsa
  • Yayin da ya ziyarci jihar Neja, shugaban kasar ya ce ba halayyarsa ba ce ɗora wa gwamnatin da ta shuɗe laifin rashin tsaro da matsin tattalin arziki
  • Shugaba Tinubu ya ce aikinsa shi ne ɗaukar nauyi tare da sauya fasalin kasar nan domin haɓaka tattalin arziki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Minna, jihar Neja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa ba ya cikin ɗabi'arsa zargin tsohuwar gwamnatin da ta shuɗe dangane kalubalen tattalin arziki da rashin tsaro.

Tinubu ya ayyana kudirinsa na ɗaukar matakan da suka dace wajen saita tattalin arziki da kuma aiki tuƙuru domin kawo ci gaba ga ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta gano shirin ƴan bindiga na kai hare-hare makarantu a jihohi 14, ra faɗi sunaye

Shugaba Tinubu ya zare kansa daga zargin Buhari.
Ana ta kace-nace kan gwamnatin Buhari da gwamnatin Tinubu Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Muhammadu Buhari
Asali: Twitter

Shugaban ƙasar ya yi wannan ƙarin haske ne a Minna, babban birnin jihar Neja yayin kaddamar da shirin noma domin magance karancin abinci ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buhari vs Wale Edun: Tinubu ya tsame kansa

Idan baku manta ba wasu mukarraban Bola Tinubu sun zargi gwamnatin Muhammadu Buhari ta tsawon shekaru takwas da hannu a halin da Najeriya ke ciki yanzu.

Ɗaya daga cikin manyan makusantan Tinubu da suka cacccaki Buhari shi ne Wale Edun, ministan kuɗi da tattalin arziki.

Amma a kalamansa, shugaba Tinubu wanda ya gaji Buhari a Mayun 2023, ya ce ba halinsa bane ɗora laifi kan tsohuwar gwamnatin da ta shuɗe.

Sai dai a cewarsa, aikinsa shi ne fara ɗaukar matakan kawo sauyi da ɗora ƙasar kan turbar nasara da kwanciyar hankali, Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya tuna da talakawa, ya rage farashin kayan hatsi saboda azumi

Shugaba Tinubu ya ce:

"Idan ka duba jaridu, za ka ga wasu daga cikinmu sun shiga ruɗani ko su zagi gwamnati mai ci ko gwamnatin da ta shuɗe, ko kuma suyi uzuri domin gina gobe mai kyau."

Buhari ya yabawa Bola Tinubu

A wani rahoton kuma Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya samu babban yabo daga magabacinsa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Buhari ya yi nuni da cewa shugaban ƙasan yana iyakar bakin ƙoƙarinsa duk kuwa da ƙorafe-ƙorafen da ƴan Najeriya ke yi na halin matsin tattalin arziƙi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262