Peter Obi da Babbar Jam'iyyar Adawa a Najeriya Sun Shiga Sabuwar Matsala
- Rikicin da ya dabaibaye shugabancin jam'iyyar adawa ta Najeriya, Labour Party ya sake ɗaukar sabon salo
- Wata ƙungiya ta buƙaci kotun tarayya da ke Abuja da ta soke rajistar jam’iyyar LP ta kuma hana jam’iyyar tsayar da ƴan takara a kowane zaɓe
- Ƙungiyar ta ci gaba da cewa tun da jam’iyyar ta kasa gudanar da taronta na ƙasa tun 2019, ya kamata a soke ta
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - An buƙaci babbar kotun tarayya da ke Abuja ta soke rajistar jam’iyyar Labour Party (LP).
Wata ƙungiya ta fara yunƙurin ganin an soke rajistar jam'iyyar Labour Party a Najeriya ne, bisa dalilin cewa ta keta kundin tsarin mulkin ƙasar nan.
An kai ƙarar jam'iyyar LP a kotu
Ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/301/2024, ta kuma buƙaci kotun da ta haramtawa jam’iyyar ci gaba da tsayar da ƴan takara a duk wani zaɓe da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ke gudanarwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata ƙungiya ce dai ƙarƙashin 'Incorporated Trustees of Center for Reform and Public Advocacy', ta shigar da ƙarar a kotun da ke Abuja.
Kamar yadda jaridar Vanguard ta kawo rahoto, waɗanda ake ƙara a ƙarar sune; hukumar INEC, LP, shugaban jam'iyyar, Julius Abure da kuma shugaban ɗayan tsagin jam'iyyar, Lamidi Apapa.
Me ya sa ƙungiyar ke son a soke rajistar LP?
Masu shigar da ƙarar sun shaida wa kotun cewa jam'iyyar ta saɓa tanadin kundin tsarin mulkin shekarar 1999 na Najeriya da kundin tsarin mulkinta, bayan ta kasa kiran babban taronta na ƙasa tun shekarar 2019, cewar rahoton jaridar The Guardian.
Masu shigar da ƙarar sun kuma fadawa kotun cewa ya kamata Abure da Apapa su bi tsarin doka a matsayinsu na shugabannin jam'iyyar.
Ƴan sanda sun cafke shugaban LP
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sandan Najeriya, sun yi caraf da shugaban jam'iyyar Labour Party (LP) na ƙasa, Julius Abure.
Abure ya shiga hannu ne a yayin da ake tsaka da zarginsa kan yin sama da faɗi da kuɗaɗen jam'iyyar.
Asali: Legit.ng