Ke Butulu Ce, Matar Tsohon Gwamnan APC Ta Soki Surukarta Kan Goyon Bayan Gwamna Mai Ci
- Yayin da ake tunkarar zaben jihar Ondo, an fara samun matsalolin siyasa a jihar tun kafin zaben fitar da gwani
- Uwar gidan marigayi tsohon gwamnan jihar, Betty Akeredolu ta caccaki surukarta kan nuna goyon baya ga Gwamna mai ci
- Wannan rikita-rikita na zuwa ne kwanaki kadan bayan binne tsohon gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ondo - Uwar gidan marigayi tsohon gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredoluta ta caccaki surukarta kan goyon bayan Gwamna Lucky Aiyedatiwa.
Matar marigayin mai suna Betty Akeredolu ta soki Funke Akeredolu Aruna kan goyon bayan gwamnan yayin da ake tunkarar zaben jihar.
Gwamnan Ondo: Menene Betty ke cewa kan surukarta?
Betty ta bayyana hakan ne a shafin Instagram inda ta soki Aruna kan goyon bayan Lucky yayin da ake shirin zaben tsaida gwani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Funke ta rike mukamin mataimakiyar daraktan tsare-tsare a gwamnatin marigayi Rotimi Akeredolu.
Har ila yau, ana zargin Funke ce ta fara tona asirin rashin lafiyar marigayi tsohon gwamnan kafin rasuwarsa.
Betty ta bayyana Funke a matsayin marar kunya inda ta wallafa hoton Funke dauke da hula da ke cewa "I'm Lucky" ma'ana ina tare da Lucky.
"Wannan ita ce 'yar uwar Rotimi, Funke Akeredolu Aruna, ita ce tsohuwar hadimar Aketi.
"Marar kunya ta bayyana kanta da cewa tana tare da Lucky, maci amana, lokaci zai tabbatar idan ta na da sa'a.
- Betty Akeredolu
Wannan na zuwa ne yayin da ake shirin gudanar da zaben tsaida gwanin jam'iyyu da dama a jihar a zaben da za a yi.
Jamiyyar APC dai ta sha alwashin bai wa kowa damar neman tikiti ba tare da nuna goyon baya ga kowa ba.
An binne tsohon Gwamnan Rotimi
Kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Ondo ya gamu da Ubangijinsa bayan an birne shi a jihar a makon da ya wuce.
Gwamnan ya rasu ne a ranar 27 ga watan Disamba a kasar Jamus bayan ya sha fama da jinya.
Mutuwar tasa ke da wuya aka rantsar da mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa a yammacin ranar ba tare da bata lokaci ba.
Asali: Legit.ng