Shugaba Tinubu Ya Gamu da Cikas a CBN, Wanda Ya Naɗa Ya Yi Watsi da Muƙamin Kan Abu 1
- Urum Kalu, wanda shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya naɗa a matsayin darakta a babban bankin Najeriya CBN ya ƙi karɓan mukamin
- Sanata Orji Kalu ne ya bayyana haka yayin tantance waɗanda aka naɗa a zauren majalisar dattawa ranar Alhamis, 29 ga watan Fabrairu
- Tsohon gwamnan jihar Abia ya ce wanda aka naɗa wanda ya fito daga mazaɓarsa ya kira shi a waya ya ce muƙamin zai ci karo da aikinsa a bankin duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Ɗaya daga cikin mutanen da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa a matsayin daraktoci a babban bankin Najeriya (CBN) ya watsa masa ƙasa a ido.
Mista Urum Kalu Eke, wanda Tinubu ya naɗa a matsayin mamban majalisar daractocin CBN, ya ƙi amsar muƙamin, inda ya ce ya riga ya fara aiki a bankin duniya.
Hakan ya fito fili ne a zaman majalisar dattawan Najeriya na ranar Alhamis lokacin da ta fara aikin tantance wadanda aka nada, cewar rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar 13 ga watan Fabrairu ne shugaban kasa Tinubu ya mika sunayen Urum da wasu mutane hudu domin tabbatar da su a matsayin mambobin majalisar gudanarwa ta CBN.
Yayin tantance su yau, tsohon gwamnan jihar Abia, Sanata Orji Kalu, (APC, Abia Arewa) ya shaidawa majalisar cewa Mista Urum ya gaya masa ba zai karɓi muƙamin ba.
Meyasa ya ƙi karɓan mukami daga Tinubu?
Sanata Kalu ya bayyana cewa mutumin, wanda Tinubu ya ɗauko daga shiyyar Kudu maso Gabas kuma ɗan mazaɓarsa, ya kira shi a waya ya faɗa masa ba zai amsa ba
A rahoton Vanguard, Kalu ya ce:
"Wanda aka naɗa ya faɗa min wannan muƙamin zai ci karo da aikinsa na mai ba da shawara ga bankin duniya da hukumomin Gwamnatin Tarayya da sauran kamfanoni masu zaman kansu."
Wane mataki majalisa ta ɗauka kan sauran mutum 4?
A halin yanzu majalisar dattawa ta tabbatar da nadin sauran mutum 4 a matsayin mambobin majalisar gudanarwa ta CBN waɗanda shugaban kasa ya mika mata.
Wadanda aka tabbatar a ranar Alhamis a matsayin daraktocin CBN sune Robert Agbede, Ado Yakubu Wanka, Farfesa Murtala Sabo Sagagi da Muslimat Olanike Aliyu.
Shin Emefiele ya cancanci a yaba masa?
Rahoto ya zo cewa duk da zarge-zargen da ke kan tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya samu yabo daga wata kungiyar a Najeriya.
Kungiyar, Agbor Stakeholders Forum ta ce ba a taba samun shugaban bankin da ya kawo sauye-sauye a fannin tattalin arziki kamar shi ba.
Asali: Legit.ng