Shugaba Tinubu Ya Rantsar da Kwamishinan NPC, Ya Shiga Muhimmin Taro da Jiga-Jigai a Villa
- Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Olayinka Oladunjoye a matsayin kwamishinan hukumar ƙidaya ta ƙasa NPC ranar Litinin, 26 ga watan Fabrairu
- Jim kaɗan bayan haka shugaban kasar ya shiga taron majalisar zartarwa (FEC) a Aso Villa da ke birnin tarayya Abuja
- Taron dai ya samu halartar manyan kusoshin gwamnati da suka haɗa da SGF, George Akume da NSA Malam Nuhu Ribadu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya rantsar da Olayinka Oladunjoye a matsayin kwamishinan hukumar ƙidaya ta tarayya (NPC).
The Nation ta tattaro cewa bayan bikin rantsarwan, Shugaba Tinubu ya shiga taron majalisar zartarwa ta ƙasa (FEC) a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja yau Litinin.
Oladunjoye ta kasance tsohuwar kwamishinar ilimi, kasuwanci da harkokin hadin gwiwa a jihar Legas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta maye gurbin Misis Bimbo Salu-Hudeyin, wadda gwamnatin jihar Legas ƙarƙashin Gwamna Babajide Sanwo-Olu ta nada a muƙami a baya-bayan nan.
Sabuwar kwamishinar NPC, Oladunjoye, ta yi alkawarin yin aiki tare da duk masu ruwa da tsaki, musamman wajen amfani da fasahohin zamani domin gudanar da ƙidaya mai inganci.
Bola Tinubu na jagorantar taron FEC a Villa
A halin yanzu, Bola Tinubu na jagorantar taron majalisar zartarwa FEC na mako-mako a gidan gwamnatin tarayya da ke Abuja.
Taron dai ya sami halartar shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, mai bada shawara kan tsaron ƙasa, Nuhu Ribaɗu ɗa sakataren gwamnati (SGF), George Akume.
Haka nan kuma shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya, Dakta Folashade Yemi-Esan, na cikin ƙusoshin gwamnati da aka gani a wurin taron wanda ke gudana yanzu haka.
Manyan jiga-jigan da ba su halarci taron ba
Sai dai ƙaramar ministar birnin tarayya Abuja, Dakta Mariya Mahmoud, wadda gidanta ya kama da wuta, ba ta samu halartar zaman FEC ba yau Litinin.
Sauran kujerun da aka hanga babu kowa a zauren taron sun haɗa da ministan kwadago, Simon Lalong, wanda ya yi murabus da kuma dakatacciyar ministar jin ƙai, Betta Edu.
Atiku zai ƙara neman takarar shugaban ƙasa a 2027?
A wani rahoton kuma An samu saɓanin ra'ayoyi a jam'iyyar PDP dangane da raɗe-raɗin cewa Atiku Abubakar na da burin neman takarar shugaban ƙasa a 2027.
Wannan lamarin ya jawo damuwa kan yawan shekarunsa da ƙoshin lafiya a lokacin, wanda ya haddasa saɓani tsakanin jiga-jigan PDP.
Asali: Legit.ng