Tsohon Shugaban Kasa Ya Ce Sun Batawa Yan Najeriya Lokaci, Ya Fadi Tsarin Mulkin da Ya Dace da Kasar

Tsohon Shugaban Kasa Ya Ce Sun Batawa Yan Najeriya Lokaci, Ya Fadi Tsarin Mulkin da Ya Dace da Kasar

  • Cif Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban kasar Najeriya ya bayyana hanya daya da za a kawo karshen matsalar tattalin arziki
  • Obasanjo ya ce dawo da mulki da arzikin kasa daga Gwamnatin Tarayya zuwa jihohi da kananan hukumomi shi ne mafi kyau
  • Wannan na zuwa ne yayin da wasu ‘yan Majalisu 60 suka bukaci juya tsarin mulkin kasar zuwa na Fira Minista don samun sauki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana tsarin da ya kamata a mulki Najeriya.

Obasanjo ya ce idan ana son inganta tattalin arziki dole a karkatar da mulki da arziki daga Gwamnatin Tarayya zuwa jihohi da kananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Dakarun noma: Gwamnati ta dauki mataki 1 na tsare manoma daga farmakin 'yan bindiga

Obasanjo ya fadi tsarin mulkin da ya kamata a dauko a yanzu a Najeriya
Obasanjo ya bukaci tarwatsa tsarin da ake gudanar da mulki a yanzu. Hoto: Olusegun Obasanjo.
Asali: Getty Images

Menene Obasanjo ke cewa kan tsarin mulki?

Tsohon shugaban kasar ya ce wannar ce hanya kadai da za ta tabbatar da an dakile matsalin tattalin arziki da ake ciki a yanzu, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Olusegun ya ta’allaka matsalar rashin samar da abubuwan amfani a kasar da rashin gudanar da arzikin kasar yadda ya kamata.

Ya ce rarraba karfin iko da arzikin kasa zuwa gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi zai rage gasar da ake a sama tare da samar da abin da ake nema a kasa.

Shawarar da Obasanjo ya bayar kan tsarin mulki

Cif Obasanjo wanda ya samu wakilcin tsohon gwamnan Neja, Dakta Babangida Aliyuya bayyana haka yayin bikin kaddamar da wani littafi, Tribune ta tattaro.

A cewarsa:

“Shekaru 24 da aka yi ana gudanar da tsarin shugaban kasa bai haifar da ɗa ai ido ba a Najeriya.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban kasa ya fadi matakin da ya kamata 'yan Najeriya su 'dauka kan mulkin Tinubu

“Abu mafi amfani shi ne rarraba arzikin kasa da mulki daga Gwamnatin Tarayya zuwa jihohi da kuma kananan hukumomi.”

Dantata ya fadi tsarin mulki da ya fi dacewa

Kun ji cewa shahararren dan kasuwa a Kano, Alhaji Aminu Dantata ya bayyana tsarin mulkin da ya fi dacewa da Najeriya.

Dantata ya ce tsarin mulkin Fira Minista shi ne mafi kyau da kasar musamman a halin da ake ciki yanzu.

Dan kasuwar ya bayyana haka yayin da wasu daga cikin ‘yan Majalisun Tarayya suka ziyarce shi a Kano a makon da ya gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.