Jam'iyyar APC Ta Samu Ƙarin Ƴan Majalisu Biyu a Majalisa, Sun Karɓi Rantsuwar Kama Aiki

Jam'iyyar APC Ta Samu Ƙarin Ƴan Majalisu Biyu a Majalisa, Sun Karɓi Rantsuwar Kama Aiki

  • Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta samu ƙarin ƴan majalisu a zauren majalisar dokokin jihar Delta bayan kammala zaben cike gurbi
  • Hakan ya biyo bayan rantsar da ƴan majalisu biyu da suka samu nasara a kotun ɗaukaka ƙara da kuma zaɓen cike gurbi a inuwar APC
  • Kakakin majalisar, Honorabul Guwor, wanda ya shaida rantsuwar sabbin mambobin, ya taya su murna tare da tabbatar da shugabanci na gari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Delta - Jam'iyyar All Progressive Congress (APC) ta samu ƙarin mambobi a majlisar dokokin jihar Delta sakamakon hukuncin kotun ɗaukaka ƙara.

Shugaban majalisar dokokin, Honorabul Emomotimi Guwor, ya rantsar da sabbin ƴan majalisu guda biyu na jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

An samu asarar rayuka bayan jami'an tsaro sun yi kazamin artabu da 'yan ta'adda a jihar Arewa

APC ta samu ƙarin yan majalisa a Delta.
Jam'iyyar APC Ta Samu Karin Mambobi Biyu a Majalisar Dokokin Jihar Delta Hoto: Official APC
Asali: Twitter

Waɗanda aka rantsar ɗin sun haɗa da Honorabul Anthony Alapala, mamba mai wakiltar Bututu ta 1 da Honorabul Blessing Achoja, mamba mai wakiltar Ethiope ta Yamma a majalisar dokokin jihar Delta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dukkan ƴan majalisun biyu mambobin APC ne kuma sun karɓi rantsuwar kama aiki ne bayan kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar musu da nasara a watan Janairu.

Jaridar Leadership ta ce bisa rantsar da su, adadin ƴan majalisar APC a majalisar dokokin jihar Delta ya ƙaru zuwa bakwai yayin da PDP ke da rinjaye mambobi 22.

Majalisa ta taya sabbin mambobin murna

Jim kaɗan bayan kammala rantsar da su, kakakin majalusar, Emomotimi Guwor ya taya su murna bisa nasarar da suka samu a zaɓen da aka ƙarisa kwanan nan.

Ya kuma tabbatar da cewa majalisa ta takwas ƙarƙashin jagorancinsa za ta yi bakin kokari wajen kafa dokokin da zasu inganta rayuwar al'ummar jihar Delta.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya fusata kan kisan babban jigo a APC, ya ba jami'an tsaro muhimmin umarni

Da yake hira da ƴan jarida jim kadan bayan kammala zaman, mamba mai wakiltar Ethiope ta Yamma, Honarabul Blessing Achoja, ya yabawa mazauna mazaɓar bisa ganin ya dace ya wakilce su a majalisa.

Achoja ya yi amfani da wannan dama wajen tabbatar wa al’ummar mazabar Ethiope ta yamma cewa zasu samu wakilci mai inganci.

Bugu da ƙari ɗan majalisar ya bayyana nasarar da ya samu a matsayin wacce Allah ya ba shi.

Wane mataki kotu ta ɗauka kan Kwankwaso a NNPP?

A wani rahoton kuma Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar NNPP a zaben 2023, Rabiu Kwankwaso, ya samu nasara a kotu kan dakatarwan da aka masa.

Babbar kotun jihar Kano ta kuma hana wasu jiga-jigan NNPP daga bayyana kansu a matsayin shugabannin jam'iyya na rikon kwarya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262