Kujerar sakataren PDP na ƙasa ta fara tangal-tangal yayin da shugabanni suka faɗi wanda suke so
- Taƙaddama kan wanda zai maye gurbin kujerar sakataren jam'iyyar PDP ta ƙasa ta ƙara tsananta yayin da Kudu maso Gabas suka juyawa Anyanwu baya
- Jagororin jam'iyyar PDP na shiyyar Kudu maso Gabas sun bayyana wanda suke son ya gaji kujerar duba da tsarin karɓa-karɓa da kundin tsarin doka
- Sun bayyana cewa Sanata Samuel Anyanwu ya yi murabus daga kujerar lokacin da ya nemi takarar gwamnan jihar Imo a zaben da ya wuce
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Rigingimun da suka ɓarke kan wanda zai karɓi kujerar sakataren jam'iyyar PDP na ƙasa ya ƙara tsananta a jiya Talata, 20 ga watan Fabrairu.
Shugabannin babbar jam'iyyar adawa na shiyyar Kudu maso Gabashin Najeriya sun yi fatali da Sanata Samuel Anyanwu, kamar yadda The Nation ta tattaro.
Jagororin PDP na shiyyar sun kuma ayyana cikakken goyon bayansu ga Sunday Ideh-Okoye a matsayin wanda ya dace ya maye gurbin sakataren jam'iyya na ƙasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Karƙashin jagorancin gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, shugabannin sun buƙaci kwamitin ayyuka na ƙasa (NWC) da sauran masu faɗa a ji su yi abinda ya dace.
Sun nemi NWC da masu ruwa da tsaki su tabbatar da naɗin Udeh-Okoye a wannan kujera duba da tsarin karba-karɓa, kwansutushin na PDP da umarnin kotu, rahoton PM News.
A cewarsu, shugabancin jam’iyyar PDP na kasa ya yi watsi da matsayin shiyyar Kudu maso Gabas wanda ta kasance tungarta tun 1999 har zuwa yau.
Sun ƙara tabbatar da cewa ba za su lamurci ci gaba da da jinkiri wajen amincewa da Udeh-Okoye a matsayin sakataren jam'iyya na kasa ba.
Meyasa suke son a sauya sakataren PDP?
Sun yi ikirarin cewa Anyanwu ya yi murabus saboda ya shiga zaben gwamnan jihar Imo a matsayin dan takarar jam’iyyar PDP inda ya sha kaye a hannun Gwamna Hope Uzodimma.
Wannan na cikin abubuwan da suka cimma a wurin taron shugabannin PDP na Kudu maso Gabas wanda aka yi a jihar Enugu karkashin Gwamna Mbah.
Mbah ya ce:
"Mun rike tutar PDP gamgam a Kudu maso Gabas tare da alfahari, don haka idan muka haɗu da murya ɗaya muka ce mun yanke shawara ba tare da saɓa doka ba, ina ga kuskure ne a yi fatali da mu."
Oyo ta dakatar da basaraken gargajiya
A wani rahoton na daban Gwamnatin jihar Oyo karkashin shugabancin Gwamna Seyi Makinde ta dakatar da babban basarake na yankin ƙaramar hukumar Saki ta Yamma.
Baale na Ilua ya rasa kujerarsa ne saboda zargin da hannunsa a rikicin da ya ɓarke tsakanin garuruwan Ilua da Gbepakan.
Asali: Legit.ng