Ba a Gama Takaddamar Zaben Edo Ba, Ganduje Ya Sake Shiga Sabuwar Matsala a Jam'iyyar APC

Ba a Gama Takaddamar Zaben Edo Ba, Ganduje Ya Sake Shiga Sabuwar Matsala a Jam'iyyar APC

  • Muƙamin Abdullahi Umar Ganduje na shugabancin jam'iyyar APC na ƙasa ya fara tangal-tangal bayan an nemi ya yi murabus
  • Ƙungiyar NCRM ta jam'iyyar APC ta buƙaci Shugaba Tinubu da ya umurci Ganduje ya yi murabus daga shugabancin jam'iyyar
  • Ƙungiyar ta yi barazanar cewa idan ba ayi wani abu kan buƙatar ta ba nan da sa'o'o 96 za ta mamaye hedikwatar jam'iyyar APC ta ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wata ƙungiya a jam’iyyar APC mai suna North-Central Reality Movement (NCRM), ta yi kira ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya umurci Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya gaggauta murabus daga muƙaminsa.

Ƙungiyar tana son Ganduje ya yi murabus daga muƙamin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa bayan kammala wa'adinsa na tsawon watanni shida, cewar rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Mai ajiyar kudin jam'iyyar adawa da aka dakatar ta yi sabuwar fallasa kan shugaban jam'iyya

An bukaci Ganduje ya yi murabus
Kungiyar NCRM ta bukaci Tinubu ya umurci Ganduje ya yi murabus Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Facebook

Shugaban ƙungiyar Alh. Muhammad Ibrahim, ya yi wannan kiran ne yayin ganawa da manema labarai a Abuja ranar Talata, 20 ga watan Fabrairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce an yi ta yaɗa jita-jita cewa Ganduje na yunƙurin sanya wa a tsawaita wa’adinsa na shugabancin jam'iyyar.

Ya ci gaba da cewa, duk wani yunƙuri na dawwamar da Ganduje a kan kujerar shugaban jam’iyyar APC na ƙasa fiye da wa’adin watanni shida, zai yi hannun riga da yarjejeniyar da aka cimma tun da farko.

Meyasa ƙungiyar take so Ganduje ya yi murabus?

A cewarsa an cimma yarjejeniya ne kan cewa Ganduje zai riƙe shugabancin jam'iyyar ne na watanni shida, inda daga nan ne za a mayar da muƙamin zuwa yankin Arewa ta Tsakiya domin kammala wa'adinsu.

Ku tuna cewa magabacin Ganduje, Sanata Abdullahi Adamu wanda ya fito daga shiyyar Arewa ta tsakiya, ya yi murabus kwatsam daga muƙaminsa a shekarar 2023, watanni kaɗan bayan rantsar da Shugaba Tinubu a matsayin shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Labari mai dadi: FG ta fara biyan albashin malaman jami'a na ASUU da aka rike, bayanai sun fito

Ƙungiyar ta buƙaci shugaba Tinubu da sauran shugabannin jam’iyyar da su yi kira ga Dr. Ganduje da ya bar kujerar a mutunce domin a shirye suke su mamaye sakatariyar jam’iyyar APC ta ƙasa nan da sa’o’i 96 masu zuwa idan ba a yi komai ba.

Jaridar Vanguard ta ce ko a kwanakin baya wasu matasa na jam'iyyar APC, sun yi kira ga Shugaba Tinubu da ya sa Ganduje ya yi murabus.

APC Ta Yi Babban Kamu a Jihar Kwara

A wani labarin kuma, kuma kun ji cewa jam'iyyar APC ta yi babban kamu a jihar Kwara bayan wasu jiga-jigai a jam'iyyar PDP sun sauya sheƙa zuwa cikinta.

Daga cikin waɗanda suka sauya sheƙar akwai tsohon mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kwara, Honorabul Abubakar Suka Baba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng