Tinubu Ya Nada Surukinsa a Matsayin Shugaban Hukumar FHA
- An nada Oyetunde Oladimeji a matsayin manaja kuma shugaban Hukumar Kula da Gidaje na Tarayya (FHA)
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Ojo a ranar Alhamis, 15 ga watan Fabrairu, cikin wata sanarwa da Ajuri Ngelale ya fitar
- Ojo tsohon dan majalisar wakilai na tarayya ne kuma shine mijin Folashade Tinubu-Ojo, iyaloja na jihar Legas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Gidan gwamnati, Abuja - A ranar Alhamis, 15 ga watan Fabrairu, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin surukinsa, Oyetunji Oladimeji Ojo, a matsayin sabon shugaba kuma direkta na Hukumar Gidaje na Tarayya (FHA).

Asali: Twitter
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, Ojo, wanda tsohon dan majalisar wakilai na tarayya ne, yana auren babban 'yar Tinubu, Misis Folashade Tinubu-Ojo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai bada shawara na musamman ga shugaban kasa kan watsa labarai Ajuri Ngelale, a ranar Alhamis, ya sanar da nadin Ojo da wasu shugabannin hukumomin gwamnati karkashin Hukumar Tarayya ta Gidaje da Cigaban Birane.
A cewar sanarwar, Shugaba Tinubu ya nada Mista Shehu Usman Osidi a matsayin manaja kuma shugaban Bankin Bada Bashin Gidaje na Tarayyar Najeriya (FMBN).
An kuma nada manyan direktoci uku na FMBN.
Sune:
1. Mista Ibidapo Odojukan, Babban Direkta (Kudi da Ayyukan Hukuma)
2. Mista Muhammad Sani Abdu, Babban Direkta (Bashi da Ayyukan Bashin Gidaje); da
3. Miss Chinenye Anosike, Babban Direkta (Cigaban Kasuwanci da Sassa)
An kuma nada wasu manyan direktoci hudu na FHA.
Sune:
Mista Mathias Terwase Byuan, Babban Direkta (Harkokin Gidaje da Akawun)
Mista Umar Dankane Abdullahi; Babban Direkta (Cigaban Kasuwanci)
Injiniya Oluremi Omowaiye, Babban Direkta (Aiwatar da Ayyuka); da
Arc. Ezekiel Nya-Etok, Babban Direkta (Harkokin Kula da Rukunin Gidaje).
Asali: Legit.ng