Ganduje Ya Yi Wa Atiku da Jam'iyyar Kwankwaso Babban Lahani a Birnin Abuja
- Dubban magoya bayan jam'iyyun adawa guda huɗu sun tattara kayansu sun koma jam'iyyar APC mai mulki a birnin tarayya Abuja
- Magoya bayan PDP, NNPP, Labour Party da PRP akalla 6,000 sun ce sun zabi komawa APC ne saboda yadda ta ɗauko mulkin Najeriya
- Darakta Janar na ƙungiyar magoya bayan APC, Farfesa Kailani Muhammad, ya ce za a haɗa hannu da kowa domin gina ƙasar da kowa zai alfahari da ita
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta ƙara nakasa manyan jam'iyyun adawa PDP, NNPP, Labour Party da People’s Redemption Party (PRP).
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa dubban magoya bayan waɗannan jam'iyyu guda huɗu da ba su gaza 6,000 ba sun sauya sheƙa zuwa APC mai mulki a birnin tarayya Abuja.
Darakta Janar na ƙungiyar magoya bayan APC (CASG), Farfesa Kailani Muhammad, ne ya bayyana haka a wani taron kamfe a Abuja ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, sauya sheƙar waɗannan mutane na nuna yadda ƴan Najeriya suka aminta cewa jam'iyyar APC ce ɗaya tilo da ke ƙara musu karfin guiwa da fatan samun sauyi.
Farfesa Muhammad ya ce:
"Wannan taro na maraba da waɗannan dandazon masu sauya sheka alama ce da ke nuna yadda ƴan Najeriya suka ankara cewa APC ce kaɗai jam'iyyar da ke ƙara musu fata."
Gwamnatin APC zata kawo ƙarshen matsaloli
Muhammad ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu tana aiki tukuru wajen ganin an shawo kan matsalolin da suka addabi kasar nan.
"Muna tabbatar wa ƴan Najeriya cewa komai mai wucewa ne saboda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta APC ta tsara dabarun magance duk wata barazana ga kokarin kawo ci gaba."
Da yake tsokaci man masu sauya shekar kuma, DG ya ƙara da cewa za a tafi da kowa domin gina kasar da kowa zai yi alfahari da ita.
A nasu ɓangaren, masu sauya shekar sun ce sun shiga APC ne saboda jagoranci mai ma'ana da Shugaba Tinubu da gwamnonin APC suka ɗauko a faɗin kasar nan.
Tinubu ya faɗi wata magana mai daɗi a taron gwamnoni
A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci gwamnoni su biiya ma'akatansu bashin albashin da suke bi kuma su biya fansho da giratutin masu ritaya.
Shugaban ƙasar ya bayyana haka a wurin ganawarsa da gwamnonin jihohi ranar Alhamis, 15 ga watan Fabrairu, 2024 a Aso Villa.
Asali: Legit.ng