Shugaba Tinubu Ya Faɗa Wa Gwamnoni Abu 1 da Zasu Yi Domin Kuɗi Su Yawaita a Hannun Jama'a

Shugaba Tinubu Ya Faɗa Wa Gwamnoni Abu 1 da Zasu Yi Domin Kuɗi Su Yawaita a Hannun Jama'a

  • Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci gwamnoni su biiya ma'akatansu bashin albashin da suke bi kuma su biya fansho da giratutin masu ritaya
  • Shugaban ƙasar ya bayyana haka a wurin ganawarsa da gwamnonin jihohi ranar Alhamis, 15 ga watan Fabrairu, 2024 a Aso Villa
  • Tinubu ya buƙaci gwamnonin su biya waɗannan kuɗaɗen domin mutane su samu walwala inda ya ce, "ku kashe kuɗi amma kar ku kashe mutane"

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ranar Alhamis, 15 ga watan Fabrairu, 2024, ya roƙi gwamnonin Najeriya su kashe kuɗaɗe amma banda mutane.

Shugaban ƙasar ya yi wannan furucin ne a wurin taron gaggawan da ya yi da gwamnonin jihohin Najeriya yau Alhamis a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Jerin gwamnonin da suka halarci ganawa da Shugaba Tinubu kan tsadar abinci da muhimmin abu 1

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
"Ku kashe kuɗaɗe amma kada ku kashe mutane" Shugaba Tinubu ga gwamnoni Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar The Nation tattaro cewa ɗaya daga cikin batutuwan da aka kawo a wurin taron shi ne biyan bashin albashin ma'aikatan gwamnati da haƙƙin ma'aikatan da suka yi ritaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake tsokaci kan wannan batu, Bola Tinubu ya roƙi gwamnonin su tabbata sun biya ma'aikata basussukan albashin da suka biyo gwamnatocin su.

Ya kuma roƙi gwamnonin su yi duk mai yiwuwa wajen biyan ƴan fansho haƙƙinsu da giratutin waɗanda suka yi ritaya.

Shugaba Tinubu ya ce haka zai taimaka wajen yawaitar kuɗi a hannun al'umma tun da a halin yanzu jihohi suna samun maƙudan kudi daga asusun tattara haraji da kasafi FAAC.

A kalaman da aka ji shugaban ƙasar ya faɗawa gwamnonin ya ce, "ku kashe kuɗaɗe amma kada ku kashe jama'a."

FG da Gwamnoni sun amince da kafa ƴan sandan jihohi

Bugu da ƙari, a wannan taron, Shugaba Tinubu da gwamnoni sun amince da kafa rundunar ƴan sandan jihohi da nufin kawo ƙarshen matsalar tsaro a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu da gwamnoni sun fara shirin ɗaukar mataki 1 da zai magance matsalar tsaro a Najeriya

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris, yayin hira da ƴan jarida bayan taron, ya ce yanzu za a fara zaman tsara yadda za a kafa ƴan sandan.

Jerin gwamnonin da suka gana da Tinubu

A wani rahoton kuma Bola Tinubu ya yi ganawar gaggawa da gwamnonin jihohi kan muhimman batutuwan da suka taso musamman tsaro da tsadar rayuwa.

Legit Hausa ta tattaro muku gwamnonin da suka samu damar halartar wannan zama da aka yi a fadar shugaban ƙasa ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262