Tsadar Rayuwa: Shugaba Tinubu Ya Caccaki Gwamnonin PDP, Ya Fadi Abu 1 da Ya Kamata Su Yi
- Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta caccaki gwamnonin adawa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP bisa kalaman da suke yi kan halin ƙuncin da ake ciki
- Tinubu, ta bakin ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Muhammed Idris, ya bukaci gwamnonin da su bayar da bayani kan abin da suka yi da ƙarin kason da suka samu
- A cewar ministan, gwamnonin sun ƙi mayar da hankali wajen yin abin da ya kamata a matsayinsu na mambobin majalisar tattalin arziƙi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja – Shugaban gwamnatin tarayya Bola Tinubu ya ƙalubalanci gwamnonin da aka zaɓa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP da su yi wa ƴan Najeriya bayani kan ƙarin kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ke ba su.
Gwamnatin Tinubu ta yi wannan tsokaci ne a lokacin da take mayar da martani ga matsayar gwamnonin adawa, waɗanda suka ɗora alhakin taɓarɓarewar tattalin arziƙin ƙasar nan kan gwamnatinsa.
Gwamnonin PDP sun yi zargin cewa manufofin tattalin arziƙin Tinubu, sun jawo wa ƙasar nan wahala da yunwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya caccaki gwamnonin PDP
Sai dai, a wani saƙo da ma’aikatar yaɗa labarai ta wallafa a shafinta na twitter, Shugaba Tinubu, ta hannun ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya caccaki gwamnonin.
Ministan ya buƙaci gwamnonin da su fito su yi wa ƴan Najeriya bayanin abin da suka yi da ƙarin kuɗaɗen da suka samu daga gwamnatin tarayya.
Ministan ya yi zargin cewa gwamnonin PDP da dama ana binsu bashin albashi da fansho duk da ƙarin kason da suka samu.
Ya ce da yawa daga cikinsu ba su taɓuka wani abin da zai bunkasa noma a jihohinsu ba, sai dai kawai su juya suna zargin gwamnatin tarayya.
Me FG ta ce kan gwamnonin PDP?
Wani ɓangare na bayanin Idris na cewa:
"Yayin da ake sa ran ƴan adawa za su yi siyasa, ya kamata a yi hakan a cikin iyakokin gaskiya da hujjoji.
"Bai kamata Gwamnonin PDP su sauya gaskiya tare da ba ƴan Najeriya bayanan da ba su ba ne haƙiƙnin halin da ƙasarmu ke ciki.
"Tun daga lokacin da Shugaba Tinubu ya hau kan karagar mulki, kudaden shiga da ake samu a matakai uku na gwamnati ya ninka fiye da ninki biyu.
"Dukkanin jihohi 36 da suka haɗa da ƙananan ƙukumomi 774, suna samun kaso mai tsoka, bayan sauye-sauyen da Shugaba Tinubu ke yi na sake fasalin tattalin arziƙin ƙasarmu.
"Ya kamata ƴan Najeriya su tambayi gwamnonin PDP yadda suka yi amfani da ƙarin kuɗaɗen shigar da suka samu wajen inganta rayuwar ƴan Najeriya a jihohinsu."
Na Hannun Daman Atiku Ya Soki Masu Zagin Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Daniel Bwala, tsohon mai magana da kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar, ya kare Shugaba Tinubu kan tsadar rayuwar da ake fama da ita a ƙasar nan.
Bwala ya yi bayanin cewa masu sukar shugaban ƙasar ya kamata su sani cewa, matsalar hauhawar farashin kayayyaki ta shafi duniya ne gabaɗaya ba Najeriya kawai ba.
Asali: Legit.ng