Jam'iyyar APC Ta Gama Shiri, Ta Faɗi Jiha 1 da Zata Ƙwace Mulki Daga Hannun Gwamnan PDP a 2024
- Jam'iyyar APC ta jaddada cewa lokaci ya yi da za ta ƙwato mulkin jihar Edo daga ranar 12 ga watan Nuwamba, 2024
- Muƙaddashin shugaban APC na jihar, Jarret Tenebe, ne ya bayyana haka yayin hira da manema labarai ranar Litinin a sakateriya da ke Benin
- Ya kuma taya ƴan takarar gwamna 12 da aka tantance kuma ya ba su tabbacin cewa za a ba kowa damar fafatawa a zaben fidda gwani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Muƙaddashin shugaban jam'iyyar APC na jihar Edo, Jarret Tenebe, ya bayyana cewa jam'iyyar ta shirya tsaf domin komawa kan madafun ikon jihar a watan Nuwamba.
Mista Tenebe ya ce APC zata yi duk mai yiwuwa ba tare da saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasa 1999 da dokar zaɓe 2022 ba wajen lashe zaɓen gwamnan da za a yi a Edo.
Ya kuma bada tabbacin bai wa kowane ɗan takara dama daga cikin ƴan takara 12 da jam'iyyar ta tantance domin su fafata a zaben fidda gwani ranar 17 ga watan Fabrairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tenebe ya yi wannan jawabi ne ranar Litinin, 12 ga watan Fabrairu a sakateriyar jam'iyyar APC da ke titin filin jirgi a Benin, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
APC ta aike da saƙo ga yan takara 12
A kalamansa, shugaban APC na jihar ya ce:
"Jam'iyyar APC reshen jihar Edo na baiwa dukkan ƴan takarar gwamna 12 tabbacin cewa za a samar musu da filin murza wasa domin gudanar da sahihin zaɓen fidda gwani.
"Ta hanyar wannan zaɓe na cikin gida ne APC ke fatan tsaida wanda zai jagorance ta wajen lashe babban zaɓen gwamna ranar 21 ga watan Satumba, 2024.
"Muna taya dukkan waɗannan ƴan takara murnar tsallake matakin tantancewa kuma APC ta jihar Edo ba ta ware guda ɗaya ta goya masa baya ba gabanin zaben fidda gwani."
A ƙarshe, Mista Tenebe ya roƙi magoya bayan jam'iyyar da su jajirce wajen haɗa kai da zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya domin samun nasara a zaɓe mai zuwa cikin sauƙi, PM News ta rahoto.
Yaushe za a samu saukin tsadar kayan abinci a Najeriya?
Rahoto ya zo cewa Ƴan kasuwa a jihar Kano sun amince zasu rage farashin kayan masarufi yayin ganawa da shugaban hukumar yaƙi da rashawa, Muhyi Magaji.
Shugaban ƴan kasuwar, Ibrahim Ɗanyaro, ya ce hauhawar farashin da ake samu kamfanoni ne suke yi amma su suna nan kan tsohon farashi.
Asali: Legit.ng