Goodluck Jonathan Ya Yi Magana Kan Abin Bakinci 1 Game Da Rasuwar Yayarsa
- Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonatahn ya ce abin bakin ciki dangane da rasuwar yayansa shine mahaifiyarta mai shekaru tana jimamin rasuwarta
- Jonathan ya ce yana Landan, a Birtaniya yayin da Madam Obebhatein Jonathan ta mutu tana da shekaru 70 a duniya
- Ya yi kira ga malaman addini da sauran 'yan Najeriya su saka mahaifiyarsa a addu'a domin juyayin rashin 'yarta
Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe
Otuoke, Jihar Bayelsa - Tsohon Shugaban Kasar Najeriya ya ce mutuwar babban yayansa Madam Obebhatein Jonathan ya jefa mahaifiyarsu, Mama Eunice Afeni-Jonathan cikin juyayin rashi.
Jonathan ya ce wani abin bakin ciki game da mutuwar marigayiyar yayansa shine cewa rasuwar ya bar mahaifiyarsu cikin damuwa, The Punch ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana hakan ne a wurin jana'izarta a Otuoke a karamar hukumar Ogbia na Jihar Bayelsa a ranar Juma'a 16 ga watan Fabrairu.
Jonathan, wanda ya ce a Landan, babban birnin Birtaniya ya samu labarin mara dadi, ya yi kira ga 'yan Najeriya su cigaba da yi wa mahaifiyarsa addua.
Ya ce:
"Yaya ta ta rasu a lokacin da za mu iya tara wadannan mashahuran mutanen don taya ta murna, amma kasancewar mahaifiyarmu na zaman makokinta shine abin bakin ciki.
"Mahaifiyata ta rasa 'yarta na farko da ya kamata ta yi zaman makokinta idan Allah ya kirata. Ina son mika godiya ta musamman ga First Lady na Bayelsa da sauran mata da suka tafi wurinta lokacin ina Landan.
"Idan ka san ta a baya da yadda ta ke a yanzu, za ka san cewa har yanzu tana cikin juyayin rashi. Don haka ku cigaba da yi wa mahaifiyata addu'a. Allah zai mana jagora. Nagode."
GEJ: Tsohon Shugaban Ƙasa Ya Yi Babban Rashi a Najeriya
Tunda farko kun ji cewa Dr Goodluck Ebele Jonathan, tsohon shugaban kasa ya yi babban rashi yayin da yayarsa, Madam Obebhatein Jonathan, ta riga mu gidan gaskiya.
Ƴar uwar tsohon shugaban ƙasar ta rasu ne ranar Alhamis, 11 ga watan Janairu, 2024 a babban asibitin tarayya FMC da ke Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.
Marigayya Madam Obebhatein ta mutu ne bayan fama ta jinya ta ƙanƙanin lokaci tana da shekaru 70 a duniya, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Asali: Legit.ng