Jigo: Kwankwaso Zai Ɗare Kujerar Shugaban Kasa a 2027 Idan Tinubu Ya Yi Kurkure 1 Tal
- Babban jigon NNPP ya bayyana kuskuren da gwamnatin APC zata yi wanda zai buɗe wa jam'iyyar Kwankwaso kofar lashe zaben 2027
- Ambasada Ajadi ya ce idan har APC ta gaza cika buri da muradan Najeriya to cikin sauƙi talakawa zasu juya mata baya a zaɓe na gaba
- A cewarsa, jam'iyyar APC ta kasa kawo sauyi mai kyau a ɓangaren tsaro da sauran ɓangarorin da suka addabi mutane
Jihar Kano - Wani babban ƙusa a New Nigeria People’s Party, (NNPP), Ambasada Olufemi Ajadi Oguntoyinbo, ya yi hasashen yadda NNPP za ta kai labari a zaben 2027.
Jigon ya bayyana cewa idan har gwamnatin APC karkashin Bola Ahmed Tinubu, ta gaza cika buri da fatan ƴan Najeriya, hakan zai buɗe wa NNPP ƙofar nasara a zabe na gaba.
Mista Ajadi ya yi wannan furucin ne a daidai lokacin da jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ta lashe zaɓen cike gurbi na ƴan majalisar dokoki 2 a jihar Kano.
Kamar yadda Tribune ta ruwaito, Ambasada Ajadi ya ce jam'iyyar NNPP na aiki tuƙuru ba kama hannun yaro kuma ita zata lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan baku manta ba INEC ta ayyana NNPP a matsayin wacce ta lashe zaɓe a mazaɓu biyu cikin uku da aka gudanar a Kano ranar Asabar da ta gabata, cewar jaridar Blueprint.
Taya jam'iyyar Kwankwaso zata kai labari a 2027?
Ajadi ya ci gaba da cewa ‘yan Najeriya na takaicin yadda jam’iyyar APC ke mulkin ƙasa, yana mai cewa talakawa sun haƙura ne suna jiran 2027 ta zo su kawar da APC daga mulki.
Ya ce gazawar APC wajen ɗaga darajar Najeriya da kuma yadda cin hanci da rashawa ya zama ba komai ba a gwamnatin jam'iyyar ne zai tuntuɗa NNPP zuwa ga nasara.
Ya jaddada cewa jam’iyyar APC ta gaza magance kalubalen da suka addabi al'umma kamar wutar lantarki mara inganci, rashin isassun wuraren kiwon lafiya, da kuma fama da yunwa.
A kalamansa ya ce:
"Ba wai batu ne na siyasa kaɗai ba a'a, magance matsalolin da ke addabar kasar nan, wadanda APC ba ta iya tunkararsu ba."
Mun jin raɗaɗi kamar kowane ɗan kasa - Abbas
A wani rahoton kuma Majalisar wakilai ta yi magana kan tsadar rayuwa, rashin tsaro da sauran wahalhalun da ƴan Najeriya suka tsinci kansu a ciki.
Shugaban majalisar, Tajudeen Abbas, ya ce shi da sauran ƴan majalisa suna shan radadi irin wanda al'umma ke sha a yanzu.
Asali: Legit.ng