Majalisar Tarayya Ta Bayyana Mataki Mai Kyau da Ta Ɗauka Domin Share Hawayen Ƴan Najeriya

Majalisar Tarayya Ta Bayyana Mataki Mai Kyau da Ta Ɗauka Domin Share Hawayen Ƴan Najeriya

  • Majalisar wakilai ta yi magana kan tsadar rayuwa, rashin tsaro da sauran wahalhalun da ƴan Najeriya suka tsinci kansu a ciki
  • Shugaban majalisar, Tajudeen Abbas, ya ce shi da sauran ƴan majalisa suna shan radadi irin wanda al'umma ke sha a yanzu
  • Ya ce majalisar za ta yi duk mai yiwuwa wajen taimakawa gwamnatin tarayya a warware dukkan waɗannan kalubale

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban majalisar wakilan tarayya, Abbas Tajuddeen, ya ce majalisa na jin radaɗin da ƴan Najeriya ke ji yayin da rayuwa ta yi tsada a ƙasar nan.

Abbas ya kuma bayyana cewa majalisar tana tare da su a fafutukar neman samun ingantacciyar rayuwa, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An shiga rudani kan batun mutuwar babban basarake a Najeriya, an fadi gaskiyar abin da ya same shi

Kakakin majalisar wakilan tarayya, Abbas Tajudeen.
"Muna tare da yan Najeriya kuma muna shan wahalar da suke sha" In ji Abbas Hoto: HouseNGR
Asali: Facebook

Ya yi wannan furucin ne a wurin taron manema labarai na duniya wanda ya gudana a birnin tarayya Abuja ranar Alhamis, 8 ga watan Fabrairu, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane mataki majalisar za ta ɗauka?

Ya ce majalisar wakilai ba ta manta da matsalolin rashin tsaro da ke kara ta’azzara a faɗin kasar ba.

A cewarsa, za su yi duk mai yiwuwa domin ganin majalisa ta taimaka wa gwamnati wajen samar da ingantacciyar rayuwa ga al’ummar Najeriya.

Shugaban majalisar ya ƙara da cewa a yanzu ƴan Najeriya na cikin jarabawa amma ya jaddada cewa duk da haka jajircewa da haɗin kan kasa ba zai taɓu ba.

Ya ce kaddamar da jiragen helikwafta na yaki guda biyu da sojoji suka yi wata alama ce da ke nuna cewa gwamnati ta kuduri aniyar magance matsalolin tsaro.

Bugu da ƙari, Abbas ya nanata cewa majalisar wakilai ba zata kama hannu ta zuba ido ba, za ta bada duk abin da ake buƙata daga gare ta domin taimakawa gwamnati.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro: Birnin tarayya Abuja na fuskantar babbar barazana, majalisar dattawa ta magantu

Ya ce taron tsaro da majalisar ta shirya yi nan gaba, ta kirkiro shi ne da nufin hada kan masana domin yin nazari da lalubo hanyoyin da za a bi wajen kawar da duk wani kalubalen tsaro a kasar nan.

Shin farashin fetur zai kara tashi nan kusa?

A wani rahoton kuma Kamfanin mai na ƙasa NNPCL ya musanta rahoton da ke yawo cewa farashin man fetur zai ƙara tashi a Najeriya.

Ya kuma shawarci masu ababen hawa da su kaucewa sayen mai da haɗa cunkoso a gidan mai saboda tsoron ƙara farashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel