A Karshe, Ƙungiyoyin Jihohi 19 Sun Bayyana Matsayar Arewa Kan Mulkin Shugaba Tinubu
- Arewacin Najeriya na nan tare da Gwamnatin Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu duk da halin tsadar rayuwar da ake ciki
- Ƙungiyoyin kare martabar demokuraɗiyya ne suka bayyana haka a wani taron manema labarai da suka kira a Abuja yau Alhamis
- Sun bayyana cewa gwamnatin Bola Tinubu na kokarin magance kalubalen da ta gada daga Muhammadu Buhari
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Wasu ƙungiyoyi masu rajin kare demokuraɗiyya na jihohi 19 da ke Arewacin Najeriya sun yi magana kan gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Ƙungiyoyin sun haɗa baki sun bayyana cewa Arewacin Najeriya na goyon bayan Shugaba Tinubu duk da wahalhalu da ƙuncin rayuwar da aka shiga, The Nation ta ruwaito.
Sun kuma yi tir da zanga-zangar da wasu mutane suka gudanar a jihohin Arewa da sunan adawa da tsarukan gwamnati mai ci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyoyin sun yi kira ga jama’a da su kasance masu hakuri da baiwa shugaban kasa hadin kai yayin da yake kokarin kawar da kalubalen da ya gada.
Gamayyar kungiyoyin daga jihohin Arewa 19, karkashin 'Arewa Initiative for the Defence and Promotion of Democracy (AIDPD)' ne suka faɗi haka a taron manema labarai a Abuja.
Kungiyoyin sun yabawa ƴan Najeriya
Shugaban kungiyoyin, Farfesa Shehu Abdullahi Ma’aji, ya yabawa ‘yan Arewa masu kishin kasa da sauran ‘yan Najeriya da suke bada hadin kai da goyon bayan gwamnati mai ci a yanzu.
Ya jaddada cewa gwamnatin shugaba Tinubu, "ta gaji matsaloli da dama daga gwamnatin da ta shude ta Muhammadu Buhari wadda a halin yanzu take kokarin magancewa."
Vanguard ta rahoto shugaban ƙungiyoyin na cewa:
"A yanzu tattalin arzikin duniya ya taɓu saboda yaƙin da ke wakana tsakanin Rasha da Ukraine da kuma Isra'ila da Gaza, mun fahinci cewa Najeriya ba shafaffa da mai bace.
"Gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta gaji matsaloli da dama daga tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari wanda a halin yanzu take kokarin magancewa.
"Alal misali gwamnan Kwara kuma shugaban gwamnonin Najeriya ya ce ɗanyen man da ƙasar zata samu daga nan zuwa watanni 6 masu zuwa, an siyar da su tun a mulkin Buhari.
"Saboda haka mun fahimci ba za a magance matsalolin farat ɗaya ba dole sai an bi a hankali a hankali."
Gwamnati za ta ɗauki malamai 5000
A wani rahoton kuma Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya amince da ɗaukar sabbin malamai 5,000 da kuma ma'aikatan ilimi 250 a jihar.
Sakataren watsa labaran gwamnan, Olawale Rasheed, ya ce tuni gwamnati ta umarci ma'aikatar ilimi ta fara bin matakan da ya dace.
Asali: Legit.ng