Rigima Ta Ƙara Tsananta a APC Yayin da Mutum 2 Suka Ayyana Kansu a Matsayin Shugaban Jam'iyya

Rigima Ta Ƙara Tsananta a APC Yayin da Mutum 2 Suka Ayyana Kansu a Matsayin Shugaban Jam'iyya

  • Rikicin APC a jihar Benuwai ya ɗauki sabon salo yayin da mutum 2 suka ayyana kansu a matsayin shugabannin jam'iyya
  • Sakataren walwala na jihar, Benjamin Omakolo, ya ayyana kansa a matsayin muƙaddashin shugaban APC na jihar
  • Haka nan kuma dakataccen shugaban jam'iyyar na asali ya jaddada cewa yana nan daram a kujerarsa, lamarin ya kai ga tashin hankali

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Rigingimun cikin guda da suka dabaibaye jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Benuwai sun bude sabon babi.

Channels tv ta kawo rahoton cewa a halin yanzun mutum ne suka yi iƙirarin shugabancin APC ta jihar da ke Arewa ta tsakiya.

Jam'iyyar PDP ta dare gida biyu a Benue.
Rudani Yayin da Mutum 2 Suka Ayyana Kansu a Matsayin Shugaban APC a Jihar Benue Hoto: OfficialAPC
Asali: Twitter

Hakan ta faru ne bayan dakataccen sakataren walwala, Benjamin Omakolo, ya ayyana kansa a matsahin muƙaddashin shugaban APC na jiha bayan dakatar da Austin Agada.

Kara karanta wannan

An shiga rububi, Gwamnatin Tinubu ta magantu kan yadda za ta daga darajar Naira a kan dala

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Agada dai ya shiga matsala ne bayan gundumarsa, Owukpa Ehaje, ta dakatar da shi daga matsayin shugaban APC na jiha.

Wannan taƙaddama dai da ke kara tsananta a APC mai mulki ya haddasa lalata babbar sakateriyar jam'iyyar da ke birnin Makurɗi.

An lalata kayyaki masu amfani a sakateriyar APC

Daraktan kiwon lafiya da fasahar sadarwa na jam’iyyar APC na jihar, Martinez Tyotsumeh, ya zargi gwamnatin Benuwai da jagorantar ‘yan sanda da sojoji wajen kai farmaki sakateriya.

A cewarsa, sojoji da ƴan sanda sun lalata motoci, kayayyakin ofis, kwamfutoci, wayoyi kana kuma suka yi awon gaba da makudan kuɗin da za a ba wakilan APC a zaben cike gurbi na Guma 1.

Sai dai kuma batun dakatarwan da aka yi wa sakataren walwala wanda yanzu yake ikirarin shi ne muƙaddashin shugaban APC, ya zo da tangarɗa yayin da jagororin gundumarsa suka ƙaryata lamarin.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta ƙara yin garambawul, ta naɗa sabon mataimakin shugaban jam'iyya na ƙasa

Sun zargi kwamitin gudanarwa na jihar da na ƙaramar hukumar Apa da sa hannun bogi domin dakatar da sakataren walwalar jam'iyyar na jiha, Leadership ta ruwaito.

Rikicin neman jan ragamar APC ta jihar Benuwai tsakanin magoya bayan Gwamna Alia da sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, ya ƙara kamari ranar 1 ga watan Fabrairu.

A lokacin ne hadiman gwamnatin Benue suka jagoranci jami'an tsaro suka farmaki ƴan jarida a taron manema labarai a sakatariyar jam'iyyar.

Kwankwanso zai maida hankali kan tsaro

A wani rahoton kuma Alamu na kara nuna cewa Kwankwaso bai haƙura da neman mulkin Najeriya ba kuma zai iya sake fitowa takara a zaben 2027

Jigon NNPP kuma ɗan takarar sanata a 2023, Farfesa Geoff Onyejegbu, ya faɗi abu 1 da tsohon gwamnan zai baiwa fifiko idan ya ƙarbi mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262