INEC Ta Dakatar da Zaɓen Cike Gurbin da Ake Yi a Kano da Wasu Jihohi 2, Ta Jero Dalilai
- Hukumar INEC ta dakatar da zaben cike gurbin da ke gudana yau a mazaɓu uku na jihohin Kano, Enugu da Akwa Ibom
- A wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar, INEC ta ce ta ɗauki wannan matakin ne saboda rikici, kura-kurai da sace jami'an zaɓe a jihohin uku
- Yau 3 ga watan Fabrairu, 2024, INEC ke gudanar da zaɓen cike gurbi da sauran ƙarishen zabe a jihohi 26
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta dakatar da zaben cike gurbin da ake yi a yau Asabar a wasu mazabun jihohin Kano, Enugu da Akwa Ibom.
INEC ta bayyyana cewa ta ɗauki wannan matakin ne saboda tashe-tashen hankula, tafka kura-kurai da kuma garkuwa da wasu jami'an zaɓe.
Mazaɓun da matakin ya shafa sun hada da mazabar jihar Enugu ta kudu 1 a jihar Enugu, mazabar tarayya Ikono/Ini a jihar Akwa Ibom da kuma Kunchi/Tsanyawa a jihar Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da INEC ta wallafa a shafinta na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter mai ɗauke da sa hannun kwamishinan yaɗa labarai, Sam Olumekun.
Meyasa INEC ta dakatar da zaɓukan?
A cewar INEC, "an dakatar da zaɓe a rumfunan zabe 8 na mazaɓar Enugu ta kudu 1 sabida masu kaɗa kuri'u basu tantance ainihin takardar sakamakon zaben ba kafin a fara zabe."
A Akwa Ibom kuma, INEC ta dakatar da zaben ne a rumfuna biyu, 003 a ƙaramar hukumar Ini da 003 a ƙaramar hukumar Ikono, sabida ƴan daba sun sace kayan zaɓen.
A mazabar Kunchi/Tsanyawa ta jihar Kano, INEC ta ce an dakatar da zaɓen a dukkan akwatu 10 da ke karamar hukumar Kunchi sakamakon farmaki, barna da kuma tada hargitsin da ‘yan daba suka yi.
An tsaurara tsaro a Kano
A wani rahoton kuma kun ji cewa an tsaurara matakan tsaro a rumfunan zaben da zaɓen cike gurbi ke gudana yau a mazaɓun ƴan majalisar dokoki 3 a Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa mutane sun fito suna kaɗa kuri'a cikin kwanciyar hankali ba tare da tangarɗa ba.
Asali: Legit.ng