Jam'iyyun Siyasa 4 Sun Rushe Tsarinsu, Sun Koma Bayan Ɗan Takarar APC a Zaɓen Kaduna

Jam'iyyun Siyasa 4 Sun Rushe Tsarinsu, Sun Koma Bayan Ɗan Takarar APC a Zaɓen Kaduna

  • All Progressives Congress (APC) ta ƙara samun gagarumin goyon baya yayin da ake shirye-shiryen zaɓen cike gurbi a jihar Kaduna
  • A mazaɓar mamba mai wakiltar Chikun a majalisar dokokin Kaduna, jam'iyyu 4 sun rushe tsarinsu, sun koma bayan ɗan takarar APC
  • Ƴan takarar waɗannan jam'iyyu sun bayyana cewa ayyukan alherin gwamna ne suka ja hankalinsu suka ɗauki wannan matakin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Chikun, jihar Kaduna - Yayin da ake shirye-shiryen ƙarisa zaɓe a mazaɓar mamba mai wakiltar Chikun a majalisar dokokin Kaduna, APC ta kara tada komaɗa.

Ƴan takara hudu a mazaɓar Chikun na jam'iyyun siyasa daban-daban sun fasa shiga zaben, sun ayyana goyon bayansu ga Jesse Tanko na jam'iyyar APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Atiku ya bayyana ƴan takarar da yake goyon baya a zaben da za a yi ranar Asabar a jihohi 9

Gwamna Malam Uba Sani.
Kaduna: Jam'iyyu 4 Sun Janye, Sun Marawa Ɗan Takarar APC Baya a Zaben Asabar Hoto: Uba Sani
Asali: Facebook

Waɗanda suka janye takara domin marawa APC baya sun haɗa da Zipporah Bijeh na Accord Party, da David Sunday na Zenith Labour Party (ZLP).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran ƴan takara biyun sune, Idris Inuwa daga Social Democratic Party (SDP), da kuma David Batholomew na jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA).

A ranar Alhamis 1 ga watan Fabrairu, 2024, Inuwa, wanda ya wakilci dukkan ‘yan takarar hudu, ya bayyana matakin janyewa daga zaben a garin Kaduna.

Meyasa suka ɗauki wannan matakin?

Inuwa ya ƙara da cewa sun yanke wannan shawara ne bayan la'akari da yadda gwamna mai ci ya ɗauko hanyar kafa jagoranci mai inganci domin amfani al'umma.

Kamar yadda Punch ta tattaro, Inuwa ya ce:

"Mun shiga takarar nan ne domin mu wakilci Chikun da kuma samarwa al'ummar mu romon demokuraɗiyya, wanda a cikin masu neman kujerar, mun yi imani ɗan takarar APC zai iya."

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Jam'iyyar APC ta yi magana kan tsohon gwamnan arewa da ke son tsige Ganduje

Ya jaddada cewa Gwamna Uba Sani ya nuna a shirye yaje wajen kawo ci gaɓa ga jihar Kaduna tare da tabbatar da hada kan kowa.

An rantsar da mataimakin gwamnan Ondo

A wani rahoton kuma Alkalin alkalan jihar Ondo ya rantsar da sabon mataimakin gwamnan jihar, Dakta Olaide Adelami ranar Alhamis, 1 ga watan Fabrairu, 2024.

Wannan dai ya biyo bayan naɗin da Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya yi masa kuma majalisar dokokin Ondo ta amince da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel