Jerin Sunaye: Majalisar Dokoki Ta Tabbatar da Sabbin Kwamishinoni 18 da Gwamnan Arewa Ya Naɗa
- Majalisar dokokin jihar Kogi ta tabbatar da naɗin sabbin kwamishinoni 18 waɗanda sabon gwamnan jihar ya aiko mata
- A wani lamari da ba a taɓa tsammani ba, Gwamna Ododo ya sanar da naɗin kwamishinonin a jawabinsa na bikin rantsarwa
- Shugaban majalisar, Aliyu Umar Yusuf, ya ce dukkan mutanen da gwamnan ya naɗa sun cancanci yin aiki tare da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kogi - Majalisar dokokin jihar Kogi ta tantance tare da tabbatar da mutane 18 da aka nada a matsayin kwamishinonin jihar a ranar Laraba, 30 ga watan Janairu.
Sabon gwamnan jihar, Alhaji Ahmed Usman Ododo, ne ya gabatar da sunayen wadanda ya nada a matsayin kwamishinoni ga majalisar.
Leadership ta ce a wani mataki da ba a taba ganin irinsa ba, Gwamna Ododo ya sanar da sunayen sabbin kwamishinoninsa da wasu manyan mukarrabai a wurin bikin rantsar da shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ododo ya karɓi shahadar kama aiki a matsayin gwamnan jihar Kogi na biyar a tarihi ranar Asabar da ta gabata, 27 ga watan Janairu, 2024, The Cable ta ruwaito.
A wurin wannan bikin rantsuwa ne sabon gwamnan ya sanar da naɗin wasu kwamishinoni da ya ce za a tura majalisa domin tabbatar da su a matsayin mambobin majalisar zartarwa ta jiha (SEC).
Majalisar dokoki ta amince da naɗinsu
Kakakin majalisar dokokin jihar Kogi, Honorabul Aliyu Umar Yusuf, ya bukaci kwamishinonin da aka nada su yi aiki tukuru domin ci gaban jihar.
Yayin da yake karanto rahoton kwamitin majalisar, shugaban majalisar ya bayyana cewa dukkanin kwamishinoni 18 da aka nada sun cancanci yin aiki.
A cewarsa gaba ɗayansu suna da kwarewa da gogewar yin aiki a matsayin mambobin majalisar zartarwa bayan tantance su.
Jerin sunayen sabbin kwamishinonin Ododo
1. Injiniya Farouk Danlami Yusuf
2. Bariata Salami Ozigi-Deedat
3. Basiru Abubakar Gegu
4. Dakta Adams Abdulaziz
5. Injiniya Joseph Oluwasegun Stephen
6. Muizideen Yinusa Abdullahi (SAN)
7. Rabiatu Okute
8. Honorabul Kingsley Fanwo
9. Fatima Momoh
10. Injiniya Mohammed Yusuf
11. Timothy Ojoma
12. Sunday Faleke
13. Mista Abanika Taye
14. Asiwaju Idris Asiru
15. Injiniya Mohammed Adbulmutalib
16. Wemi Jones
17. Mohammed Shuaibu
18. Aridajo Monday.
Kotu ta sa a kamo CoS na gwamnan jihar Ribas
A wani rahoton kuma Kotun tarayya mai zama a Abuja ta bada umarnin damke shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar Ribas, Edison Ehie.
Mai shari'a Emeka Nwite ne ya bada umarnin kama hadimin gwamna Fubara tare da wasu mutane 5 kan kona majalisar dokokin Ribas.
Asali: Legit.ng