Atiku Ya Yi Martani Kan Hukuncin Kotun Koli a Nasarar Zaben Gwamnan PDP
- Atiku Abubakar ya yi martani kan hukumacin Kotun Koli da ta kai nasara bangaren PDP a jihar Adamawa
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana nasarar Gwamna Fintiri a matsayin gagarumar nasara ga ahlin jam'iyyar PDP
- Da yake yanke hukunci a ranar Laraba, Mai shari'a John Okoro, ya yi watsi da karar da 'yar takarar jam'iyyar APC, Aisha Dahiru Binani ta daukaka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Atiku Abubakar, 'dan takarar jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasa na 2023, ya taya Gwamna Ahmadu Fintiri murnar kan nasarar da ya samu a Kotun Koli.
Ku tuna cewa a ranar Laraba, 31 ga watan Janairu, Kotun Koli ta tabbatar da cewar Fintiri, dan takarar PDP a zaben ranar 18 ga watan Maris, 2023, shine ainahin wanda ya lashe zaben.
Wani kwamitin Kotun Koli mai mutum biyar ne ya yi watsi da karar da Aisha Ahmed Dahiru, 'yar takarar jam'iyyar APC a zaben.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake martani a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Laraba, ya jinjinawa hukuncin Kotun Kolin kan takaddamar zaben Adamawa.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana nasarar Fintiri a matsayin "karin nasara ga ahlin PDP."
Atiku ya rubuta:
"Ina taya Gwamna Ahmadu Fintiri murna, wanda Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da nasararsa a zaben gwamna na watan Maris din 2023. Hakan nasara ce ga ahlin PDP da damokradiyyar kasarmu. -AA"
Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Fintiri
A wani labarin, mun ji cewa kotun koli ta tabbatar da nasarar Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP a matsayin gwamnan Adamawa.
Kotun kolin, karkashin jagorancin Mai shari’a John Okoro, ta yi watsi da karar da Aishatu Dahiru, ‘yar takarar jam’iyyar APC ta shigar kan zaben jihar na 2023, TVC News ta ruwaito.
Mai shari’a Okoro ya bayyana cewa ayyana Dahiru a matsayin wacce ta lashe zaben da kwamishinan zabe na jihar (REC) ya yi ya sabawa doka.
Ya ce jami’in zabe (RO) ne kawai dokar zabe ta ba shi ikon bayyana sakamakon zaben, kuma duk wanda ya yi hakan ya sabawa doka.
Asali: Legit.ng