Musulmai Sun Cire Tsoro, Sun Bayyanawa Gwamnan APC Ido da Ido Bukatarsu Kan Nade-Naden Gwamnati
- Al’ummar Musulmi a jihar ondo sun koka kan yadda gwamnatin jihar ke nuna wariya karara a gare su
- Suka ce gwamnan ya yi nade-nade wadanda suka saba ka’ida tare da nuna wariya ga Musulmai da ke jihar
- Shugaban gamayyar limaman, Sheikh Ahmad Aladesawe ya bayyana haka yayin da suka kai wa gwamnan ziyarar jaje
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ondo – Gamayyar limaman jihar Ondo sun soki nuna wariya da Gwamna Lucky Aiyedatiwa ke yi wa Musulmai.
Malaman suka ce gwamnan ya yi nade-nade wadanda suke da tasiri tare da nuna wariya ga Musulmai, cewar The Nation.
Mene Musulman ke cewa?
Limaman suka ce gwamnatin da ta shude ta yi amfani da basira wurin dakile Musulman jihar da mai da su kamar ba ‘yan jihar ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun shawarci Gwamna Lucky da ya guji dukkan shawarwarin mutane ko kungiya da zai jawo kin sauraran al’ummar Musulmai.
Shugaban gamayyar limaman, Sheikh Ahmad Aladesawe ya bayyana haka yayin da suka kai wa gwamnan ziyarar jaje, cewar The Guardian.
Sheikh Aladesawe ya kara da cewa duk kokarin da suka yi don nusar da gwamnantinm da ta shude kan wariyar ya ci tura.
Ya ce:
“Mu a matsayinmu na dattawa ba ma jin dadi, matasan mu ma haka, dole muke danne su kan abubuwan da suke faruwa.
“Mun yi musu alkawarin cewa idan muka zauna da kai za ka kawo karshen wannan wariya da ake nuna mana.
“Mai girma gwamna, al’ummar Musulmai ba su ji dadin yadda ka yi nade-nade ba, ka yi nadi guda hudu dukkansu babu Musulmi a ciki.”
Martanin gwamnan kan lamarin
Gammayyar limaman har ila yau, sun tambayi gwamnan cewa babu wani Musulmi da ya cancanta ne a nada shi.
Suka ce jihar Ondo ba jihar Kiristoci ba ce inda suka ce dole a kawar da nuna wariya idan ya na so a zauna lafiya.
Sun kalubalanci gwamnan kan zaban mataimaki wanda ba Musulmi ba duk korafe-korafen da ake yi amma ya yi biris da hakan.
Yayin martaninshi, gwamnan ya ce ya yi nade-naden ne duba da siyasa ba wai don kabilancin addini ba inda ya yi alkawarin duba bukatarsu a gaba.
Gwamna Lucky ya dauki mataimaki
A wani labarin, bayan shafe wata daya kacal a kan mulki, Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo ya nada mataimaki.
Wannan na zuwa ne bayan rasuwar tsohon gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu a watan Disambar 2023.
Asali: Legit.ng