Dan Takarar Gwamna a APC Ya Yi Alkawarin Yin Wa'adi 1 Kacal a Kan Mulkin Jihar, Ya Fadi Dalilansa
- Dan takarar gwamna a jam'iyyar APC a jihar Anambra, Sanata Ifeanyi Ubah ya bayyana cewa wa'adi daya ya ishe shi a kan mulki
- Ubah ya ce duk wani gwamna mai tsari da kuma son ci gaban jiharsa shekaru hudu sun ishe shi ya saka jihar a turba mai kyau
- Ubah wanda ke wakiltar Anambra ta Kudu ya bayyana haka ne bayan nuna sha'awar tsayawa takara a zaben da za a gudanar a badi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Anambra - Sanata Ifeanyi Ubah ya yi alkawarin yin wa'adi daya kacal idan aka zabe shi a matsayin gwamnan jihar.
Ubah wanda ke wakiltar Anambra ta Kudu ya bayyana haka ne bayan nuna sha'awar tsayawa takara a zaben da za a gudanar a badi.
Mene Ubah ke cewa kan takara?
Sanatan a kwanakin baya ya fice daga jami'yyar YPP tare da komawa jamiyyar APC saboda tsayawa takarar gwamnan jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ifeanyi ya ce dole ne a saka jihar a kan turbar ci gaba ta bangaren tattalin arziki da walwalar jama'a.
Ya ce Gwamna Charles Soludo ya kashe jihar murus kamar yadda al'ummar jihar suka ce sun gaji da mulkin jami'yyar APGA, cewar Premium Times.
Dan takarar ya ce shekaru hudu sun isa duk wani gwamnan da ke son ci gaba ya daura jiharsa kan turbar ci gaba ta ko wane bangare.
Alkawuran da Ubah ya dauka
Ya yi alkawarin gudanar da zaben kananan hukumomi watanni hudu kacal da hawanshi karagar mulki a jihar idan aka zabe shi.
Sanatan ya ce zai dauki matakin ne saboda ita ce hanya kadai da za ta taimaka wurin isar romon gwamnati ko ina, cewar Vanguard.
Har ila yau, ya ce duk jama'a sun dogara cewa gwamnan a matsayinsa a Farfesa a tattalin arziki zai sauya akalan jihar.
Ya ce amma abin takaici madadin ɗaga jihar gaba a fannin tattalin arziki ya durkusar da hanyoyin samun kudade a jihar.
Ubah ya koma APC
Kun ji cewa, Sanata Ifeanyi Ubah ya watsar da jamiyyarsa ta YPP tare da komawa jamiyyar APC mai mulki.
Ubah wanda ke wakiltar mazabar Anambra ta Kudu ya sauya shekar ne yayin da ya ke neman kujerar gwamnan jihar.
Asali: Legit.ng