Kotun Ƙoli Ta Yanke Hukuncin Ƙarshe Kan Karar da Aka Nemi Tsige Shugaban Ƙasa Tinubu

Kotun Ƙoli Ta Yanke Hukuncin Ƙarshe Kan Karar da Aka Nemi Tsige Shugaban Ƙasa Tinubu

  • Wata kara da aka ɗaukaka zuwa gaban Kotun Kolin Najeriya kan nasarar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ba ta je ko ina ba daga zuwa
  • Ƙotun ta yi fatali da karar ba tare da ɓata lokaci ba, inda ta ce gaba ɗaya ƙorafin bai cancanta ba
  • Ambrose Albert Owuru, wanda ya shigar da ƙarar, ya ƙalubalanci Buhari, tsohon Antoni Janar da INEC a shari'ar wadda ta yi musun nasarar APC a 2019 da 2023

FCT Abuja - Kotun Kolin Najeriya ta kori ƙarar da aka kalubanci nasarar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a zangon mulkin da ya fara na shekara huɗu.

Kotun ta kuma kori ƙarar da aka shigar da tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, Antoni Janar na ƙasa (AGF) da hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC).

Kara karanta wannan

Atiku ya yi tsokaci kan ficewar Kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso daga kungiyar ECOWAS

Shugaba Tinubu da Buhari.
Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Kan Karar da Ta Nemi Tsige Shugaba Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Kotun ta yanke wannan hukunci ne ranar Litinin, 29 ga watan Janairu, 2024, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Idan baku manta ba Buhari ya miƙa wa Shugaba Tinubu mulki ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa kotun ƙoli ta yi wannan hukunci?

Kotun mai daraja ta ɗaya ta kori ƙarar wadda tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Hope Democratic Party (HDP), Ambrose Albert Owuru da jam'iyyarsa suka shigar, bisa rashin cancanta

Kwamitin alƙalai biyar ƙarƙashin Mai shari’a John Okoro, ya yanke cewa karar ba ta da tushe balle makama kuma ba ta cancanta ko kaɗan, wanda nan take ya kore ta.

Mai shari’a Okoro ya umurci lauyan mai kara, Habeeb Olawuyi, ya janye karar sannan kuma ya ba shi shawarar kada ya ƙara gabatar da kara irin wannan a gaban kotu.

Kara karanta wannan

Bayan dakatar da Betta Edu, an bukaci Tinubu ya kori minista kan abu 1 tak

Kotun ta umarce shi da ya biya N10m ga kowanne daga cikin waɗanda ake ƙara, Buhari, Tinubu, AGF da INEC, kamar yadda AIT ta ruwaito.

Ko meyasa Owuru ya kai Buhari da Tinubu ƙara?

Tun farko babbar kotun tarayya, ranar 30 ga watan Janairu, 2023 ta kori ƙarar tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar HDP, Owuru, wanda ya ƙalubalanci nasarar Buhari a 2019.

Mista Owuru, lauya wanda ya samu kwarewa a Burtaniya, ya shigar da ƙarar Buhari da INEC a babbar kotun tarayya ne yana rokon ta ayyana shi a matsayin wanda ya ci zaɓe.

Ya kuma roƙi kotun ta duba halastaci ko akasin haka na matakin da INEC ta ɗauka a zaben 2019, inda ata ɗage zaɓe daga ranar 16 ga watan Fabrairu, zuwa 23 ga watan Maris.

Ministan Tinubu ya musanta shiga takarar gwamna

A wani rahoton kuma Ministan bunƙasa harkokin ma'adanai na ƙasa ya nesanta kansa daga wasu fastoci masu nuna zai nemi takarar gwamnan jihar Ekiti.

Dele Alake ya ce ko kaɗan ba shi da alaƙa da fastocin kuma ba ma ya sha'awar shiga takarar gwamnan jihar a zaɓe na gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262