Ganduje Ya Fadawa Kwankwaso: Da Zarar Ka Shigo APC, Zan Zama Shugabanka

Ganduje Ya Fadawa Kwankwaso: Da Zarar Ka Shigo APC, Zan Zama Shugabanka

  • Abdullahi Umar Ganduje, shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa ya sake tsokano rikicinsa da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
  • A yayin da ake rade-radin yiwuwar dawowar Kwankwaso jam'iyyar APC, Ganduje ya aika masa da sako mai muhimmnaci
  • Ganduje ya jadada cewa shine zai zama shugaban tsohon mai gidansa idan har ya ce zai shigo APC, kamar yadda ake hasashe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Jihar Kano - Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya tunatar da kowa musamman jagoran Kwankwasiya, Rabiu Musa Kwankwaso cewa da zarar sun shigo APC, shi zai zama shugabansu.

Ganduje, a jawabin da ya yi cikin wani bidiyo da ya yadu, ya jadada cewa idan dai maganar jam'iyyar APC ake yi, shine lamba daya kuma mutum mafi muhimmanci.

Kara karanta wannan

Jigo a NNPP ya yi zancen yiwuwar hadewar Abba, Kwankwasiyya da Ganduje a APC

Ni zan zama kakanka idan ka dawo APC, Ganduje ga Kwankwaso
Ganduje ya fadawa Kwankwaso cewa shi zama mai gidansa idan ya dawo a APC. Hoto: Abdullahi Ganduje/Rabiu Kwankwaso
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto ya ce:

"Idan kana maganan APC ne mune shugabannin APC. Ba a kananan hukumomi ba, ba a jiha ba, ba shiyya ba amma a kasa baki daya.
"Idan kai dan jam'iyyar APC ne mai kati, kana karkashin shugaban jam'iyya na kasa. Haka shugabannin gunduma, jihohi da shiyoyi.
"Idan ka shigo APC yau, kana kasa da mu kuma kai mabiyinmu ne. Yana da muhimmanci ka lura da haka; dan gida da bako duk suna karkashin mai gida."

Ganduje ya tattauna da yan APC

Ganduje, wanda ya yi wa taron yan jam'iyyar APC a Kano jawabi ya yi kira gare su kada su tada hankulansu ko su ji tsoron shigowar wani jam'iyyar APC.

Har ila yau cikin jawabinsa, Ganduje ya cigaba da cewa:

"Kamar yadda na fada muku, ko kai wanene kuma duk matsayinka ko da kai jagora ne, da ka shigo APC toh akwai kakanka a nan!".

Kara karanta wannan

Kano: Ganduje ya roki Abba Gida-Gida ya shigo jam’iyyar APC

Siyasar Kano: Ganduje Ya Magantu Kan Yiwuwar Kwankwaso Ya Koma Jam'iyyar APC Su Sake Haduwa

Tun a baya, shugaban jam'iyyar APC na kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana kwarin gwiwar cewa za su sake zama inuwa daya da Rabiu Kwankwaso, jagoran NNPP na kasa.

Duk da tsawon lokacin da suka shafe suna zaman doya da manja, Ganduje ya ce ba abin mamaki bane shi da tsohon gwamnan su sake cure wa wuri daya domin dama tare suke.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel