A Karo Na Biyu, Gwamnan PDP Ya Rantsar da Sabbin Kwamishinoni 9 Bayan Sun Yi Murabus
- Gwamna Fubara ya sake rantsar da kwamishinoni 9 karo na biyu a wani biki da aka shirya a gidan gwamnatinsa da je Fatakwal
- Kwamishinonin sun yi murabus a farko domin nuna goyon bayansu ga Wike, amma daga bisani gwamnna ya sake naɗa su
- Hakan ya biyo bayan sulhun da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi tsakanin Ministan Abuja da gwamnan Ribas
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya rantsar da kwamishinoni tara da ya sake naɗawa a karo na biyu bayan sun yi murabus.
Bikin ranstuwar kama aikin kwamishinonin ya gudana ne a ɗakin taron majalisar zartarwa da ke gidan gwamnati a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.
Kwamishinonin sun yi murabus ne domin nuna goyon bayansu ga Nyesom Wike, ministan birnin tarayya Abuja a lokacin rikicinsa da Gwamna Fubara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar The Nation ta rahoto cewa sabbin kwamishinonin sun karɓi rantsuwar kama aiki, tun daga rantsuwar biyayya har zuwa rantsuwar shiga ofis.
Da yake taya kwamishinonin da aka sake rantsarwa murna, Gwamna Fubara ya bukaci su maida hankali wajen yin ayyukan da zasu zama alheri ga jihar Ribas.
Gwamnan ya yi kwamishinonin nasiha
Gwamnan na jam'iyyar PDP ya kuma roƙe su da su tabbata sun bi tanadin kundin tsarin mulki sau da ƙafa a dukkan ayyukan da zasu tasa a gaba.
A rahoton Daily Trust, Fubara ya ce:
"Ina muku fatan alheri bisa sake dawowa wannan muƙami. Ku tsaya kan adalci, ku tsayu kan muradun jiharmu. Wannan ita ce manufar nada ku a waɗannan muƙamai kuma ita ce gaskiya.
“Na ga yadda zukatanku suka yi nauyi, amma ina tabbatar muku cewa ban kullaci wani daga cikinku ba, kawai dai wutar ta rutsa da ku ne a tsakiya.
"Ina mai baku shawara ku yi iya bakin kokarinku, kamar yadda na faɗa tun farko, ku yi abinda jihar nan da jikokin mu masu zuwa zasu tuna da ku su yi alfahari."
Ganduje ya magantu kan alaƙarsa da Kwankwaso
A wani rahoton kun ji cewa Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi magana kan masu tunanin alaƙarsa da Kwankwaso ba zata yi ƙarko ba ko sun haɗu a APC
Tsohon gwamnan Kano ya ce yana da ƙwarin guiwar zasu sake haɗewa wuri ɗaya domin tun usuli a tare aka gansu
Asali: Legit.ng