Atiku Ya Yi Magana Mai Daukan Hankali Kan Nasarar Da Wasu Gwamnoni 2 Suka Yi a Kotun Ƙoli
- Alhaji Atiku Abubakar ya aike da saƙon taya murna ga gwamnonin PDP 2 da suka yi nasara a kotun ƙoli yau Alhamis
- Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Fubara na Ribas da Gwamna Kefas na Taraba a zaben 18 ga watan Maris
- Da yake martani kan nasarar, tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce wannan nasara ce ga kowane ɗan PDP
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya taya gwamnonin jihohi Taraba da Ribas murnar samun nasara a kotun ƙoli
Alhaji Atiku ya taya gwamnonin biyu na jam'iyar PDP murna ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter ranar Alhamis.
Legit Hausa ta kawo rahoton cewa kotun koli ta kori ƙarar ɗan takarar APC, Tonye Cole tare da tabbatar da nasarar Siminalayi Fubara a matsayin gwamnan jihar Ribas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan haka kuma kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Agbu Kefas a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Taraba da aka yi ranar 18 ga watan Maris.
Atiku ya aike da saƙon taya murna ga gwamnonin 2
A sakon taya murna da ya aike wa gwamnonin PDP 2, Atiku ya ce wannan nasarar da suka samu, nasara ce ga ɗaukacin ƴaƴan jam'iyyar PDP.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya rubuta a shafinsa cewa:
"Ina taya murna ga gwamnoni, Gwamna Agbu Kefas da jihar Taraba da Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas waɗanda aka tabbatar da nasarar da suka samu yau a Kotun Koli.
"Babu shakka wannan ba nasara ce kawai ta kashin kai ba, nasara ce ga dukkan ƴaƴan PDP, al'ummar Najeriya, da duk masu ƙaunar Dimokradiyya da ganin an yi Adalci.
"Haƙiƙa nasararsu ta kara karfafa gwarin guiwarmu na ɗorewar demokuraɗiyya wanda ƴan ƙasa suka fara haƙura duba da manufar APC na cin nasara ko ta halin ƙaƙa da rashin bin doka da oda."
Tsohon daraktan kamfen Atiku ya bar PDP
A wani rahoton kuma Tsohon hadimin Atiku Abubakar ya kara rikita jam'iyyar PDP yayin da ake tunkarar zaɓen gwamna a jihar Ondo
Sanata Kunlere, wanda ya wakilci Ondo ta kudu daga 2011 zuwa 2015, ya fice daga jam'iyyar PDP
Asali: Legit.ng