Yayin da Ake Murnar Lashe Zaben Kano, Uban NNPP Ya Fadi Raunin Jam’iyyar a Zaben da Za a Gunadar
- Duk da nasarar lashe zaben gwamnan jihar Kano, Jigon NNPP ya bayyana damarsu ta lashe zaben jihar Legas a yanzu
- Dakta Boniface Aniebonam ya ce a yanzu jam’iyyarsu ba ta da karfin cin zaben jihar Legas duk da nasararsu a Kano
- Uban jam’iyyar ya bayyana haka ne a yau Alhamis 25 ga watan Janairu yayin hira da manema labarai
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Uban jam’iyyar NNPP a Najeriya, Dakta Boniface Aniebonam ya bayyana karfin jam’iyyar a jihar Legas.
Boniface ya tabbas jam’iyyar duk da lashe zaben jihar Kano ya na da matukar wahala ta iya cin zabe a jihar Legas.
Mene jigon NNPP ke cewa?
Uban jam’iyyar ya bayyana haka ne a yau Alhamis 25 ga watan Janairu yayin hira da manema labarai, cewar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aniebonam ya na magana ne yayin da aka tambaye shi kan yiwuwar nasarar jam’iyyar a zaben cike gurbi da za a gudanar a watan Faburairu.
Jigon jam’iyyar ya kwatanta karfin jam’iyyar ce yayin da za a ke shirin gudanar da zaben cike gurbi a mazabar Surulere 1 a Majalisar Tarayya.
Idan ba a mantaba, Hukumar INEC ta sanya 3 ga watan Faburairu a matsayin ranar gudanar da zaben cike gurbi a kasar.
Yiwuwar cin zaben NNPP a Legas
Ya ce:
“A yanzu, zaben jihar Legas ya na da matukar muhimmanci, a gani na jam’iyyar NNPP ba ta da karfin cin zabe a Legas a halin yanzu.
“Watakila a nan gaba, za mu yi kokari muga mun yi wani abu don tabbatar da nasara a zabe a jihar Legas.”
Jam’iyyar NNPP dai ta lashe zaben gwamnan jihar Kano da ratar kuri’u masu dimbin yawa a watan Maris din shekarar 2023.
Nasarar ta bai wa Gwamna Abba Kabir Yusuf damar kasancewa gwamnan farko a Najeriya karkashin jam’iyyar, Peoples Gazette ta tattaro.
Matasan APC sun bukaci a kori Ganduje
Kun ji cewa matasan jam’iyyar APC sun bukaci Shugaba Tinubu ya sallami shugaban jam’iyyar, Umar Ganduje.
Matasan sun yi kiran ne ganin yadda Ganduje ya gagara kawo jihar a zaben da aka gudanar a watan Maris
Asali: Legit.ng