Gwamnan PDP Ya Naɗa Kwamishinoni 2 Bayan Watanni 8 a Kan Mulki, Ya Aike da Saƙo Majalisa
- Gwamna Oborevwori na jihar Delta ya naɗa sabbin kwamishinoni 2 bayan hawa mulki watanni takwas da suka wuce
- Rahoto ya nuna tun da gwamnan ya ɗare madafun iko, wannan ne na farko da ya naɗa kwamishinan yaɗa labarai da kwamishinan shari'a
- Majalisar dokokin jihar Delta ta karɓi sunayen waɗanda aka naɗa kuma ta sanya ranar tantance su a makon gobe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Delta - Bayan shafe sama da watanni takwas a kan madafun iko, Gwamna Sherrif Oborevwori ya naɗa kwamishinoni biyu da aka jima ana jira a jihar Delta.
Gwamnan na jam'iyyar PDP ya sanar da sunayen mutum biyu da ya naɗa a matsayin kwamishinan yaɗa labarai da Antoni Janar kuma kwamishinan shari'a.
Jerin sabbin kwamishinonin da Oborevwori ya naɗa
Wadanda gwamnan ya naɗa sun haɗa da sakataren watsa labaran jam'iyyar PDP reshen Delta, Dakta Ifeanyi Osuoza, a matsayin kwamishinan yaɗa labarai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai kuma Ekemejero Ohwovoriole, babban lauya a Najeriya da ya kai matakin SAN a matsayin Antoni Janar kuma kwamishinan shari'a na jihar Delta, Tribune ta tattaro.
Har ila yau, gwamnan ya sanar da nadin tsohon shugaban karamar hukumar Bomadi, Kalanama Penawou, a matsayin kwamishinan kananan hukumomi da masarautu.
Gwamna ya aika sunayensu ga majalisar dokokin jihar
Gwamna Oborevwori ya aika da sunayen waɗannan kwamishinoni da ya naɗa zuwa majalisar dokokin jihar ranar Talata, 23 ga watan Janairu, 2024.
Kakakin majalisar dokokin, Rt. Honorabul Emomotimi Guwor, ya karanta sunayen mutanen a zauren majalisar yayin zamansu na jiya Talata.
Ana sa ran kowane daga cikin wadanda aka nada zai mika kwafi 35 na kundin bayanan karatunsa (CV) ga magatakardar majalisar daga nan zuwa ranar Litinin mai zuwa.
Sannan kuma zasu bayyana a gaban majalisar domin tantnace su a makon gobe ranar Talata, 30 ga watan Janairu, 2024.
An dakatar da biyan wasu ma'aikata albashi a Kogi
A wani rahoton na daban Gwamnatin Yahaya Bello na jihar Kogi ta dakatar da biyan albashin ma'aikata 231 tun watan Nuwamban, 2023.
Shugabar ma'aikatan jihar, Hannah Odiyo, ta ce an ɗauki wannan matakin ne saboda ma'aikatan sun taka umarnin gwamnati.
Asali: Legit.ng