Kotun Kolin Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Karar Dan Takarar APC da Ke Neman a Tsige Gwamnan PDP
- Kotun Ƙoli za ta yanke hukunci kan cece-kucen da ake yi kan zaɓen gwamnan jihar Rivers na ranar 18 ga watan Maris, 2023
- An sanar da ɓangarorin da ƙarar ta shafa cewa za a yanke hukuncin ƙarshe kan lamarin a ranar Laraba
- Tonye Cole na jam’iyyar APC yana ƙalubalantar nasarar Gwamna Fubara na jam’iyyar PDP kan cewa bai cancanta ya tsaya takara ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Kotun koli ta shirya yanke hukunci kan rikicin zaɓen gwamnan jihar Rivers.
Shari’ar da ke gaban Kotun Ƙoli ta kasance tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara na jam’iyyar PDP, da Tonye Cole na jam’iyyar APC kan zaɓen gwamnan jihar Rivers da aka yi ranar 18 ga watan Maris 2023.
Gwamna Fubara zai san makomarsa a ranar Laraba
Kamar yadda BBC Pidgin ta ruwaito, mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun wacce ke jagorantar kwamitin alƙalai biyar na kotun, a makon da ya gabata ta tanadi hukunci kan ƙarar da APC da Cole suka shigar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An sanar da ɓangarorin da ke cikin shari’ar cewa za a yanke hukuncin ne a ranar Laraba 31 ga watan Janairu.
Cole na jam’iyyar APC ya gurfana gaban kotu domin ƙalubalantar nasarar da gwamnan ya samu a zaɓen gwamnan da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta gudanar a jihar.
Jaridar Thisday ta rahoto cewa yanzu sauran ƙararrakin zaɓen gwamnoni huɗu suka rage Kotun Ƙoli ta yanke hukunci a kansu.
Yadda Fubara ya doke Tonye Cole a zaɓen gwamnan Rivers
A zaben dai Fubara ya samu ƙuri'u 302,614 inda ya kayar da abokin hamayyarsa Cole wanda ya samu ƙuri'u 95,274.
Ɗan takarar na jam’iyyar APC wanda bai gamsu da sakamakon zaɓen ba, ya garzaya kotu yana zargin an tafka maguɗi.
Bai cancanci tsayawa takara ba
Ya kuma yi iƙirarin cewa gwamnan bai cancanci tsayawa takara ba saboda yana riƙe da muƙamin akanta janar na jihar lokacin da ya shiga zaɓe.
A cewar Cole, matakin na Fubara ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasar nan saboda sai ya fara yin murabus kafin ya tsaya takara.
Kotun Ƙoli Ta Yi Watsi da Ƙarar Neman Tsige Fubara
A wani labarin kuma, kun ji cewa Kotun Ƙoli ta raba gardama kan ƙarar da jam'iyyar APM ta ƙalubalanci nasarar gwamnan jihar Rivers, Simanalayi Fubara.
Kotun mai daraja ta daya a Najeriya ta ƙori ƙarar APM da ɗan takararta na gwamna, Innocent Kere suka shigar kan nasarar Gwamna Fubara.
Asali: Legit.ng