A Karshe, Gwamnan APC Ya Kori Kwamishinoni da Masu Mukamai da Mai Gidansa Ya Nada, Akwai Dalili

A Karshe, Gwamnan APC Ya Kori Kwamishinoni da Masu Mukamai da Mai Gidansa Ya Nada, Akwai Dalili

  • A karshe, gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya rusa dukkan majalisar zartarwa a jihar baki daya
  • Gwamnan ya dauki matakin ne bayan rantsar da shi a ranar 27 ga watan Disamba jim kadan bayan mutuwar Rotimi Akeredolu
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Ebenezer Adeniyan ya fitar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo - Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya rusa dukkan majalisar zartarwa a jiharsa, kamar yadda NTA News ta tattaro.

Gwamnan ya kuma rusa dukkan mukaman siyasa da suka hada da hadimai na musamman manya da kanana a jihar.

Gwamnan APC ya sallami dukkan kwamishinoni da masu rike da mukamai
Gwamna Lucky Ya Kori Kwamishinoni da Masu Mukamai. Hoto: Lucky Aiyedatiwa.
Asali: Facebook

Mene gwamnan ya ce kan sallamar?

Kara karanta wannan

Gwamnatin Plateau ta sanya dokar hana fita na tsawon awanni 24, bayanai sun fito

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Ebenezer Adeniyan ya fitar a yau Laraba 24 ga watan Janairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta bukaci dukkan wadanda aka sallama su mika takardun ofisoshinsu ga sakatarorin din-din-din a ma'aikatunsu.

Sanarwar ta ce:

"Dukkan hadimai na musamman manya da kananan duk an sallame su nan take.
"Dukkan wadanda abin ya shafa an umarce su da mika komai ga sakatarorin din-din-din a ma'aikatunsu.
"Gwamnan har ila yau, ya godewa wadanda abin ya shafa kan irin gudunmawar da suka bayar don ci gaban jihar."

Martanin gwamnan a bayan kan jita-jitar

Wannan na zuwa kasa da wata daya bayan mutuwar tsohon gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu a watan Disamba, cewar TheCable.

Gwamna Lucky ya karbi ragamar mulki ne a ranar 27 ga watan Disamba jim kadan bayan sanar da mutuwar Akeredolu.

Kara karanta wannan

Tsige yan majalisar PDP 23: Gwamnan Filato ya ziyarci Tinubu, ya yi karin bayani

Tun a kwanakin baya ake ta rade-radin cewa gwamnan zai rusa majalisar zartarwa da sauran masu mukamai.

Sai dai a martaninshi, ya ce ba zai ce komai ba a kai sannan idan lokacin ya yi jama'a za su sani.

APC ta magantu kan tikitin gwamnan Ondo

Kun ji cewa jami'yyar APC mai mulki ta bayyana matsayarta kan tikitin zaben gwamnan jihar Ondo.

Jami'yyar ta ce ba ta yi wa Gwamna Lucky Aiyedatiwa alkawarin ba shi tikitin ba hamayya ba.

Ta ce ta na bin tsarin dimukradiyya ce don haka dole kowa ya fito ya nemi tikitin ba tare da dakile sha'awar wasu 'yan takara ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.