Tashin Hankali Yayin da Sabon Rikici Ya Ɓarke Tsakanin Magoya Bayan APC da NNPP, Bayanai Sun Fito

Tashin Hankali Yayin da Sabon Rikici Ya Ɓarke Tsakanin Magoya Bayan APC da NNPP, Bayanai Sun Fito

  • Rundunar ƴan sandan Kano ta ce ta shirya gurfanar da waɗanda ta kama da aikata laifuka daban-daban bayan hukuncin kotun ƙoli
  • Rahoto ya nuna yan sanda sun ayyana wani Habibu a matsayin wanda suke nema ruwa a jallo kan rikicin siyasar da ya faru a Gaya
  • Kwamishinan ƴan sandan Kano ya ce tuni jami'ansa suka kama mutum shida da ake zargi da hannu a tada zaune tsayen

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Magoya bayan manyan jam'iyyun siyasa masu hamayya da juna a Kano na ci gaba da arangama da juna a wasu sassan jihar a ƴan kwanakin nan.

Legit Hausa ta tattaro cewa jam'iyyun NNPP mai mulki da APC na ci gaba da zaman doya da manja a jihar, duk da har yanzun ba a rasa rai sakamakon rikicin ba.

Kara karanta wannan

Ana fargabar rayukan mutane da dama sun salwanta a wani sabon rikici a jihar Arewa

Sufetan yan sanda na ƙasa, IGP Kayode.
Magoya Bayan NNPP da APC Sun Yi Arangama a Kano, Yan Sanda Sun Shiga Tsakani Hoto: PoliceNG
Asali: Twitter

A rahoton PM News, tuni kwamishinan ƴan sanda na Kano, CP Muhammed Gumel da sauran abokan aikinsa suka fara yunƙurin magance tashin hankalin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'an tsaro sun fara ɗaukar matakai na al'umma domin warware saɓanin da ke tsakanin manyan jam'iyyun biyu cikin ruwan sanyi.

Ranar Talata, 23 ga watan Janairu, 2023, CP Gumel ya ziyarci ƙaramar hukumar Gaya, inda ya gana da jagororin APC da NNPP a fadar sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim.

An gano cewa shugabannin manyan jam'iyyun biyu sun amince da rungumar zaman lafiya bayan kammala taron wanda ya shafe tsawon sa'o'i huɗu.

Yan snada na neman Habibu ruwa a jallo

A halin da ake ciki dai, rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa tana neman Habibu ruwa a jallo bisa rikicin siyasar da ya auku a Gaya wanda ya yi muni sosai.

Kara karanta wannan

An Kama Shugaban Ƙaramar hukuma da wani bisa hannu a yunkurin kashe kakakin majalisa a Arewa

CP Gumel ya yi kira ga mazauna yankin da shugabannin al’umma da su taimaka wa ‘yan sanda da bayanai masu amfani kan yadda za su kamo Habibu.

Yan sanda sun kama mutum 6

Bugu da ƙari, kwamishinan ƴan sandan ya tabbatar da kama mutum shida daga APC da NNPP, yana mai bayanin cewa a yanzu suna kan bincike, in ji rahoton Tribune.

Rundunar ƴan sandan ta ƙara da cewa ba zata lamurci duk wani tada yamutsi da zai zama barazana ga zaman lafiya a Kano ba.

An roki Abba ya sa a kama tsohon kwamishina

A wani rahoton kuma Jigon jam'iyyar APC ya bukaci gwamnatin Kano karkashin Abba Kabir Yusuf ta kama tsohon kwamishinan da ya yi barazanar kashe alƙalai.

Ɗawisu ya yi wannan kiran ne bayan kama fitaccen ɗan siyasan nan, Abdulmajid Ɗanbilki Kwamanda kan barazanar da ya yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262