Kotu Ta Yi Hukunci Kan Sahihancin Yarjejeniyar da Aka Cimma Tsakanin Wike da Gwamna Fubara

Kotu Ta Yi Hukunci Kan Sahihancin Yarjejeniyar da Aka Cimma Tsakanin Wike da Gwamna Fubara

  • Wata babbar kotun jihar Rivers ta yi hukunci kan ƙarar da dattawan jihar suka shigar suna ƙalubalantar yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Wike da Gwamna Fubara
  • Kotun ya yi fatali da ƙarar ne saboda a cewarta ba ta da hurumin sauroron ƙarar da ƙungiyar dattawan ta shigar
  • Sai dai, lauyan ƙungiyar dattawan bayan an kammala zaman kotun ya bayyana cewa za su ɗaukaka ƙara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Wata babbar kotun jihar Rivers da ke zama a Port Harcourt, babban birnin jihar Rivers, ta yi fatali da karar da ƙungiyar dattawa da shugabannin Rivers suka shigar a gabanta.

Ƙungiyar dattawan dai sun shigar da ƙarar ne suna ƙalubalantar sahihancin “yarjejeniyar zaman lafiya” wacce Shugaba Tinubu ya jagoranta tsakanin gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara da magabacinsa, Nyesom Wike.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta yi wani abun ban mamaki bayan rashin nasara a Kotun Koli

Kotu ta yi fatali da karar dattawan Rivers
Kotun ta ce ba ta da hurumin sauraron karar Hoto: Sir Siminalayi Fubara, Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

Alƙalin kotun, mai shari’a Chinwendu Nwogu, ya yi fatali da ƙarar ne bisa dalilin cewa babbar kotun jihar da ba ta da hurumin sauraren ƙarar, cewar rahoton jaridar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A lokacin da aka fara zaman kotun, lauyan masu shigar da ƙara ya bayyana cewa duk waɗanda ake ƙara a cikin lamarin har yanzu ba a kai musu sammacin kotu ba, kuma ba za a iya sauraren ƙarar ba tun da ba a sanar da duk ɓangarorin da lamarin ya shafa ba.

Wane mataki ƙungiyar dattawan za ta ɗauka?

Bayan zaman, babban lauyan masu shigar da ƙarar, Emmanuel Rukari, ya bayyana rashin jin daɗinsa kan hukuncin da babbar kotun jihar ta yanke, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Har ila yau, lauyan ƙungiyar dattawan na Rivers, Anabs Sara-Igbe, ya ce ƙungiyar za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin da babbar kotun ta yanke.

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotun Koli: Dan takarar PDP ya aike da sako mai muhimmanci bayan rigima ta barke a Arewa

Ƙungiyar dattawa da shugabannin na Rivers dai ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Jihar, Rufus Ada-George, sun yi Allah-wadai da “yarjejeniyar zaman lafiya” da ɓangarorin Fubara da Wike suka cimma bayan Tinubu ya shiga tsakani.

Sun bayyana yarjejeniyar a matsayin wacce ta kauce wa tsarin dimokuraɗiyya kuma mai illa.

Fubara Ya Faɗi Dalilin Ƙulla Yarjejeniya da Wike

A baya rahoto ya zo cewa, Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers, ya bayyana dalilinsa na amincewa da yarjejeniyar zaman lafiya tsakaninsa da magabacinsa Nyesom Wike.

Gwamna Fubara ya bayyana cewa ya amince da yarjejeniyar ne domin ganin cewa an samu zaman lafiya a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng