PDP Ta Nutse a Cikin Matsala Bayan Tsohon hadimin Atiku Ya Maka Shugabanninta a Kotu Kan Wani Dalili

PDP Ta Nutse a Cikin Matsala Bayan Tsohon hadimin Atiku Ya Maka Shugabanninta a Kotu Kan Wani Dalili

  • Rikicin PDP ya kara tsami bayan dan takarar jam'iyyar a jihar Ogun ya maka shugabannin jam'iyyar a kotu
  • Otunba Segun Sowumi wanda tsohon hadimin dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ne ya bukaci kotun ta dakatar da shugabannin jam'iyyar
  • Ya ce shugabannin jam'iyyar sun saba kundin tsarin PDP inda ya bukaci a dakatar da su daga kiran kansu shugabanninta

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon hadimin dan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya maka shugaban jam'iyyar a kotu.

Otunba Segun Sowumi ya bukaci Babbar Kotun Tarayya ta dakatar da Umar Damagun da mukarrabansa kan saba kundin tsarin jamiyyar.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya kunno kai a jam'iyyar PDP yayin da aka maka shugabanni a gaban kotun kan abu 1 tak

Tsohon hadimin Atiku ya maka shugabannin PDP a kotu
An maka jami'yyar PDP a kotu kan saba dokar jami'yyar. Hoto: Umar Damagun.
Asali: Twitter

Mene dalilin maka shugabannin PDP a kotu?

Segun ya kuma bukaci ta taka musu birki kan kiran kansu a matsayin shugabannin jam'iyyar, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sowumi wanda ya yi takarar gwamna a jami'yyar a jihar Ogun ya ce shugabannin sun cutar da PDP saboda rashin gudanar da babban taron jam'iyyar.

Ya ce tun a watan Satumbar 2022 lokacin shugabancin Iyorchia Ayu ba a gudanar da taron ba duk da bukatar haka daga mambobin jami'yyar, cewar Latest News.

Babban matsalar da rashin taron zai haifar

A cikin karar, Segun ya ce kin gudanar da babban taron saba doka ne kuma dakile niyyar masu neman takarar jam'iyyar a gaba hakan zai yi.

Yayin shigar da karar ta bakin lauyansa, Anderson Asemota ya bukaci kotun ta tilasta jami'yyar gudanar da taron tare da tattauna batutuwa tun bayan taron na karshe.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta dakatar da shugabanta, ta fadi babban dalili 1

Wannan na zuwa ne yayin da jam'iyyar ke fuskantar zabukan cike gurbi da kuma na jihohi a wannan shekara.

PDP ta caccaka Ganduje kan kalamansa a zabe

Kun ji cewa jam'iyyun adawa a Najeriya da suka da PDP da NNPP sun caccaki shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje kan kalamansa.

Jam'iyyun suka ce Ganduje shi ne babban matsalar dimukradiyya a kasar kuma ya kamata ya bai wa 'yan Najeriya hakuri.

Wannan na zuwa ne bayan Ganduje ya zargi 'yan siyasa da kawo cikas a zabuka sabanin yadda ake zargin hukumar zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.