Mambobin Majalisar Jihar APC Sun Tsige Kakakin Majalisa Kan Dalili 1 Tak, Sun Nada Sabo
- Mambobin Majalisar jihar Ogun sun tsige kakakin Majalisar jihar kan badakalar makudan kudade
- Yan Majalisar 18 daga cikin 36 suka zabi tsige kakakin Majalisar yayin zamansu a yau Talata 23 ga watan Janairu
- Rahotanni sun tabbatar cewa an tsige Oluomo kan zargin badakalar makudan kudade da kama-karya a Majalisar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ogun - 'Yan Majalisar jihar Ogun sun tsige kakakin Majalisar, Kunle Oluomo kan wasu zarge-zarge da dama.
'Yan Majalisar 18 daga cikin 36 suka zabi tsige kakakin Majalisar yayin zamansu a yau Talata 23 ga watan Janairu.
Mene dalilin tsige Oluomo a matsayin kakakin Majalisar?
Channels TV ta tattaro cewa an tsige Oluomo saboda zargin badakalar makudan kudade da kama-karya da sauran laifuka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga bisani, 'yan Majalisun sun zabi Oludaisi Elemide a matsayin sabon kakakin Majalisar ba tare da bata lokaci ba.
A watan Satumbar shekarar 2022, Hukumar EFCC ta gurfanar da Oluomo a gaban Babbar Kotun Tarayya kan badakalar naira biliyan 2.4, cewar The Nation.
Mene ake zargin Oluomo da sauran wadanda aka kama?
An gurfanar da Oluomo ne da wasu mutane uku da suka hada da Oladapo Samuel da Adeyemo Taiwo da Adeyanju Nimota Amoke kan zarge-zarge har guda 11.
Lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo ya ce wadanda ake zargin sun aikata laifukan ne a shekarar 2019 zuwa 2022.
Oyedepo ya ce lamarin ya faru ne a jihar Ogun inda ake zarginsu da sace biliyan 2.4 a asusun Majalisar jihar.
Daga bisani, kotun ta bai wa Oluomo beli yayin da ake ci gaba da shari'ar a kotun da ke jihar Legas.
Kotu ta yi hukunci kan shari'ar zaben Ogun
Kun ji cewa Kotun Koli ta raba gardama kan shari'ar zaben gwamnan jihar Ogun da ke Kudancin Najeriya.
Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Dapo Abiodun da ke jami'yyar APC a matsayin gwamnan jihar.
Har ila yau, kotun ta yi watsi da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar PDP, Ladi Adebutu kan rashin gamsassun hujjoji.
Asali: Legit.ng