Jam'iyyar PDP Ta Dakatar da Shugabanta, Ta Fadi Babban Dalili 1

Jam'iyyar PDP Ta Dakatar da Shugabanta, Ta Fadi Babban Dalili 1

  • Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Kogi ta dauki gagarumin mataki akan daya daga cikin manyan jiga-jiganta
  • An raba Ibrahim Huseini, shugaban jam'iyyar PDP a karamar hukumar Dekina dake jihar Kogi da ayyukansa
  • Mafi akasarin jiga-jigan jam'iyyar a karamar hukumar sun kada kuri'ar tsige shugaban bisa zargin karkatar da kudade

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kogi - Jam'iyyar PDP a jihar Kogi ta dakatar da shugabanta a karamar hukumar Dekina dake jihar, Ibrahim Huseini.

An dakatar da shugaban PDP a karamar hukumar Dekina dake jihar Kogi
PDP Ta Dakatar da Shugabanta, Ta Fadi Babban Dalili 1 Hoto: Seyi Makinde
Asali: Facebook

Baya ga zamba, wasu dalilan da suka sa aka dakatar da shugaban

Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto a ranar Talata, 23 ga watan Janairu, kafin dakatarwar da aka yi wa Huseini na sai baba ta gani, an zarge shi da badakalar naira miliyan 19 daga asusun jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Kano: Yayin da rashin tsaro ya addabi Arewa maso Yamma, yan sanda sun dauki muhimmin mataki a jihar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka kuma ana zargin jigon na PDP da yin barazana ga mambobin jam'iyyar.

Jam'iyyar mai adawa a jihar ta kuma zargi shugaban nata da cin dunduniyarta a yayin zaben gwamna na watan Nuwamban 2023 da aka yi a jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata takarda mai kwanan wata 21 ga watan Janairun 2024, wanda a cikinta jiga-jigan na PDP a karamar hukumar Dekina suka kada kuri'un rashin karfin gwiwa a kansa.

Kwamitin aiki na PDP a karamar hukumar Dekina ta zargi shugaban jam'iyyar, da kin mutunta ka’idojin jam’iyyar da aka kafa.

Wani bangare na sanarwar na cewa:

"Saboda haka ana umurtanka da ka mika dukkan kayayyakin da ke hannunka ga sakataren jam'iyyar.
Ayyukanka sun kawo karan tsaye ga ci gaban jam’iyyar saboda kin bin tanadin kundin tsarin mulkin jam’iyyar.”

Kara karanta wannan

Kano: An kori daraktoci 8 a hukumar KIRS mako daya bayan Kotun Koli ta mayarwa Abba kujerarsa

Shugaban karamar hukumar ya yi martani

A halin da ake ciki, shugaban karamar hukumar ya yi martani a kan ci gaban, inda ya yi watsi da ikirarin tsige shi sannan ya bayyana cewa jami'an da suka dakatar da shi ba mambobin kwamitinsa bane.

Da yake martani ya fada ma jaridar Punch cewa:

"Wadannan sa hannun da kuke gani ba na gaske bane; jiga-jigan kwamitina sun nan daram dam. A zahirin gaskiya ma, suna da taro a ranar Laraba domin kada kuri'ar yarda da shugabancina."

PDP ta girgiza da APC a Borno

A wani labarin kuma, mun ji cewa jam’iyyar APC ta lashe zaben dukkan kananan hukumomi 27 da ke jihar Borno a Najeriya.

Har ila yau, jam’iyyar ta kuma lashe dukkan kujerun kansiloli 312 da ke wakiltar unguwanni a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng