Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Yi Martani Kan Yiwuwar Sauya Shekar Kwankwaso Zuwa APC

Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Yi Martani Kan Yiwuwar Sauya Shekar Kwankwaso Zuwa APC

  • Rahotannin cewa Rabiu Musa Kwankwaso da magoya bayansa na tunanin sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC sun mamaye shafukan intanet
  • Kwankwaso wanda tsohon minista ne, shi ne ke jagorantar tafiyar Kwankwasiyya, wacce take da ƙarfi a shiyyar Arewa maso Yammacin Najeriya
  • Da yake mayar da martani kan raɗe-raɗin cewa Kwankwaso zai iya dawowa APC, Adamu Garba ya bayyana jin ɗaɗinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar YPP, Adamu Garba, a ranar Litinin, 22 ga watan Janairu, ya yi magana kan yiwuwar sauya sheƙar Rabiu Kwankwaso zuwa APC.

Adamu Garba ya bayyana batun sauya sheƙar na Kwankwaso zuwa APC a matsayin babban kamu.

Adamu Garba ya yi martani kan yiwuwar sauya shekar Kwankwaso zuwa APC
Ana ci gaba da yada jita-jitar cewa Kwankwaso zai koma APC Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Garba, wanda jigo ne a jam’iyyar APC mai mulki, ya ce dawowar Kwankwasiyya cikin jam’iyyar APC, ci gaba ne mai kyau.

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin Buhari ya fadi dalilin da zai sanya Kwankwaso ya yi nasara a APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, shi ne ke jagorantar tafiyar siyasar Kwankwasiyya.

Tafiyar Kwankwasiyya dai ta yi fice a jihar Kano, jihar da jam'iyyar Kwankwaso ta ke mulki a halin yanzu, wato jam'iyyar NNPP.

Kwankwaso da NNPP sun zo na huɗu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 inda suka samu ƙuri’u 1,496,687.

Kwankwaso mai shekara 67 a duniya, ana yi masa kallon ɗaya daga cikin manyan ƴan siyasa masu tasiri a Najeriya.

Wane martani Adamu Garba ya yi?

Garba ya rubuta a shafinsa na X (tsohon Twitter) cewa:

"Yanzu tafiyar Kwankwasiyya za ta dawo cikin jam'iyyar APC? Wannan babban kamu ne!"

A cikin ƴan kwanakin nan dai batun sauya sheƙar Kwankwaso zuwa jam'iyyyar APC ya karaɗe shafukan sada zumunta, inda ake ta tafka muhawara a kai.

Kara karanta wannan

Hotunan Kwankwaso da Akande ya saka shakku kan makomar Sanatan, kujerar Ganduje na cikin matsala

Kwankwaso ya taɓa zama a jam'iyyar APC ƙafin ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP, inda daga bisani ya fice ya kafa jam'iyyar NNPP.

Bashir Ahmad Ya Magantu Kan Dawowar Kwankwaso APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya yi martani kan batun dawowar Rabiu Musa Kwankwaso zuwa jam'iyyar APC.

Bashir ya bayyana cewa APC za ta yi maraba da Kwankwaso tare da mabiyansa zuwa cikinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng