Kano: Jami'yyar APC Ta Yi Martani Kan Kiran Tinubu Ya Kori Ganduje, Ta Tona Asirin Kwankwasiyya
- Jami'yyar adawa ta APC a jihar Kano ta yi martani kan kiraye-kirayen korar shugaban jam'iyyar ta kasa, Dakta Abdullahi Ganduje
- Mataimakin shugaban jam'iyyar a jihar, Shehu Maigari ya yi fatali da kiraye-kirayen inda ya ce 'yan Kwankwasiyya ne suka dauki nauyinsu
- Wannan na zuwa ne bayan wasu matasan jam'iyyar APC sun bukaci Tinubu ya kori Ganduje bayan gaza yin nasara a zaben gwamnan jihar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Jami'yyar APC a jihar Kano ta yi zazzafan martani kan kiran a kori shugaban jam'iyyar, Umar Ganduje.
Jami'yyar adawa a jihar ta ce 'yan Kwankwasiyya ne suka dauki nauyin matasan APC kan wannan kira da a sauke Ganduje.
Wane kira matasan suka yi kan korar Ganduje?
Idan ba a mantaba a jiya Lahadi 21 ga watan Janairu wata kungiyar matasa ta bukaci Tinubu ya kori Ganduje daga kan kujerar shugabancin jam'iyyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matasan sun yi wannan kira ne yayin da suke zargin Ganduje da gaza yin nasara a zaben jihar da aka gudanar a watan Maris.
Shugaban kungiyar, Sadiq Ali Sango shi ya yi wannan kira a jiya Lahadi 21 ga watan Janairu a Kano, kamar yadda The Guardian ta tattaro.
Wane martani APC ta yi kan korar Ganduje?
Mataimakin shugaban jam'iyyar a jihar, Shehu Maigari ya yi fatali da kiran inda ya ce matasan ba 'yan APC ba ne.
Maigari ya ce sun sani a APC ba su da matasan da ke kiran haka, kuma shugabanninta sun san masu daukar nauyin irin wadannan, cewar Daily Trust.
Wannan na zuwa ne yayin da ake zargin akwai wani shirin hadaka tsakanin Sanata Kwankwaso da jami'yyar APC.
Jita-jitar komawar Kwankwaso APC
Kun ji cewa, Jita-jitar komawar Sanata Rabiu Kwankwaso ta kara tabbata bayan ganinsa da jigon APC, Cif Bisi Akande.
A baya, ana ta rade-radin cewa Sanatan ya yi yarjejeniya da jam'iyyar APC cewa akwai alamun ya koma jam'iyyar inda shi kuma a bangarensa ya musanta zargin.
Wannan na zuwa ne bayan samun nasara a Kotun Koli da Gwamna Abba Kabir ya yi wanda ya kasance dan jam'iyyar NNPP.
Asali: Legit.ng