Hotunan Kwankwaso da Akande Ya Saka Shakku Kan Makomar Sanatan, Kujerar Ganduje Na Cikin Matsala

Hotunan Kwankwaso da Akande Ya Saka Shakku Kan Makomar Sanatan, Kujerar Ganduje Na Cikin Matsala

  • Jita-jita na sake yaduwa kan shirin hadaka tsakanin jam’iyyar APC da Sanata Rabiu Kwankwaso bayan hukuncin Kotun Koli
  • Duk da Kwankwaso ya yi fatali da jita-jitar da cewa shi ma kwararren dan siyasa ne wanda babu wani da zai yi masa wayo
  • Sai dai wasu sabbin hotuna da aka gano Kwankwaso da jigon APC, Bisi Akande ya sake sabunta jita-jitar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Awanni kadan bayan jam’iyyar NNPP ta tabbatar da korar Sanata Rabiu Kwankwaso, akwai alamun zai iya komawa APC.

Idan ba a mantaba, tsagin jam’iyyar NNPP ta bukaci kafofin sadarwa da su rinka mutunta kundin tsarin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

A je a sasanta da Kwankwaso: Sirrin taron Ganduje, ‘yan APC da Tinubu sun fito fili

Akwai alamar ayar tambaya kan hotunan Kwankwaso da Bisi Akande
Hotunan Kwankwaso da Akande sun jefa shakku a zukatan mutane. Hoto: Concerned Nigerian.
Asali: Twitter

Wace jita-jita ake kan Kwankwaso?

Sun bayyana cewa manyan jam’iyyar kamar su Kwankwaso da sauran shugabannin kwamitin jam’iyyar korarru ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akwai jita-jitar cewa Kwankwaso ya na dasa wa da APC kwanaki kadan bayan Kotun Koli ta bai wa NNPP nasara a jihar Kano.

Wannan shi ke nuna alamun cewa akwai alamun Kwankwaso da jam’iyyar APC su kulla alaka mai karfi.

Har ila yau, Kwankwaso ya yi fatali da jita-jitar inda ya ce babu kamshin gaskiya a ciki, cewar Politics Digest.

Mene ya kara jefa shakku a zukatan mutane?

Kwankwaso ya kara da cewa shi dan siyasa ne mai ji da kansa wanda babu wani wanda zai nuna masa kwarewar siyasa da yi masa wayo.

Sai dai hotunan Kwankwaso da jigon APC, Bisi Akande suna gaisawa ya kara rura wutar jita-jitar cewa akwai alamun yarjejeniyar.

Kara karanta wannan

Bai da Amfani: A fatattaki Ganduje, a maido mana da Kwankwaso in ji Matasan APC

Ganin yadda abubuwa ke faruwa a yanzu, za a iya cewa kujerar Umar Ganduje, shugaban APC ta na cikin matsala.

APC ta sake zama a Kano bayan hukuncin Kotun Koli

A wani labarin, Jam’iyyar APC a jihar Kano ta sake zama bayan hukuncin Kotun Koli a jihar.

Jam’iyyar ta yi ganawar ce da jiga-jigan jam’iyyar a jihar don sake shiri kan tunkarar zabukan gaba a jihar.

Wannan na zuwa ne bayan Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Abba Kabir a matsayin halastaccen gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.