Bai da Amfani: A Fatattaki Ganduje, a Maido Mana da Kwankwaso In Ji Matasan APC
- Wasu matasa da ke ikirarin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC ne sun bada shawarar korar Abdullahi Umar Ganduje
- Kungiyar ta APC ta ce babu bukatar Dr. Abdullahi Ganduje ya cigaba da zama shugaban jam’iyya na kasa
- Amma shugabannin APC sun zargi ‘yan Kwankwasiyya da shigewa rigar jam’iyyar domin haifo fitina
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kano - Wasu da sunan matasan jam’iyyar APC sun yi kira ga shugabanni su tsige Abdullahi Umar Ganduje daga matsayinsa a NWC.
Tashar rediyon Freedom ta ce matasan sun bukaci a yi waje da Dr. Abdullahi Umar Ganduje saboda rashin nasarar APC a jihar Kano.
Tun da har NNPP tayi galaba a kan jam’iyya mai-ci a zaben 2023, matasan sun ce akwai bukatar a dawo da Dr. Rabiu Kwankwaso.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matasan APC sun ce a kori Ganduje
Shugaban wannan tafiya, Sadiq Ali Sango ya ce tun farko nada Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban APC ya sabawa doka.
Solacebase ta rahoto Sadiq Ali Sango yana cewa kamata ya yi shugaban jam’iyya na kasa ya fito daga yankin Arewa maso tsakiya.
Har ila yau, kungiyar ta bukaci Bola Tinubu ya guji ba tsohon gwamnan na Kano wani mukami saboda zargin taba dukiyar jama’a.
APC ta yi kira da Kwankwaso, taya Abba murna
Matasan sun yi kira ga Sanata Rabiu Kwankwaso ya shigo jam’iyyar APC domin a taimakawa jihar Kano da daukacin Najeriya.
Kungiyar ta kuma taya gwamna Abba Kabir Yusuf murnar nasarar da ya samu a kotun koli, tayi kira gare shi ya kawo cigaba a Kano.
"'Yan Kwankwasiyya ne" in ji APC
Mataimakin shugaban APC a Kano, Shehu Maigari ya ce APC ba ta da kungiya da sunan matasan nan kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Shehu Maigari ya ce ‘yan Kwankwasiyya ne suke kitsa wannan danyen aiki domin ganin bayan shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje.
Wannan shi ne ra’ayin Abdul Zulu, wani daga cikin hadiman tsohon gwamnan jihar Kano, ya ce Sango yaron Sanata Kwankwaso ne a siyasa.
NNPP: "Kwankwaso ba 'dan halal ba ne"
Ana haka kuma labari ya zo cewa jam'iyyar NNPP a Najeriya ta fitar da sabuwar sanarwa kan matsayin Rabiu Musa Kwankwaso.
Jam'iyya mai alamar kayan marmari ta ce Kwankwaso ba danta ba ne. Sanarwar ta fito ne ta bakin shugaban BOT, Temitope Aluko.
Asali: Legit.ng