2027: Akpabio Ya Shiga Matsala Yayin Da Sabon Rikicin Siyasa Ta Barke a Akwa Ibom, Bayanai Sun Fito

2027: Akpabio Ya Shiga Matsala Yayin Da Sabon Rikicin Siyasa Ta Barke a Akwa Ibom, Bayanai Sun Fito

  • Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya kasance a tsakiyar rikicin siyasa a jiharsa ta Akwa Ibom
  • An zargin cewa Akpabio na kitsa yadda zai zama wanda ke juya akalan siyasar jiharsa ta kowanne hanya har da karfi da yaji
  • A cewar masu ruwa da tsaki da kwararru a jihar Akwa Ibom, an zargi Sanata Akpabio ya ci mutuncin gwamnan farko na jihar, Obong Victor Attah

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

An gargadi Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya hakuri da duk wani shiri da ya ke yi na neman kwace ragamar siyasar jihar Akwa Ibom da karfin iko a 2027.

An fayyace masa cewa shirinsa na kwace iko a jihar ta karfi da yaji ba zai yi wu ba.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya nuna gwamnan arewa 1, ya bayyana ayyukan Alherin da Yake Zuba Wa Talakawa

Akpabio ya sha suka daga jiharsa kan zargin yana son tada rikici
An zargi Shugaban Majalisar Dattawa, Akpabio da shirin kitsa rikici a jiharsa don bukatar kwace siyasar jihar. Hoto: Godswill Akpabio
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akpabio, tsohon ministan Neja Delta, ya sha ragargaza saboda sukar da ya yi wa Obong Victor Attah, tsohon gwamnan jihar, da wasu shugabannin Akwa Ibom.

Yanzu an bukaci ya nemi afuwa saboda abin da ya aikata.

An shawarci Akpabio ya gane cewa mutanen Akwa Ibom sun rungumi hadin kai da cigaba karkashin jagorancin Gwamna Umo Eno, sunyi watsi da abin da Akapabio ya aikata a matsayin son kai da neman raba kawunan mutane.

A wani taro tare da ya yi tare da masu ruwa da tsaki, Akpabio ya yi ikirarin cewa, kafin karshen wa'adinsa a 2007, jihar ta samu cigaba mai inganci, yana mai cewa shi ya kawo manyan tagwayen tituna da sauran gine-gine.

Kungiya ta ragargaji Akpabio saboda sukar tsohon Gwamna Attah

Sai dai, a ranar Lahadi 21 ga watan Janairu, Shugaban Kungiyar na kasa, Injiniya Ufot Akan Umoren, ya fitar da sanarwa mai karfi a Abuja yana sukar Akpabio.

Kara karanta wannan

Tsige yan majalisar PDP 23: Gwamnan Filato ya ziyarci Tinubu, ya yi karin bayani

Ya soki Akpabio saboda raini abin da Gwamna Victor Attah ya yi, yana mai cewa cin fuska ne ga mafi rinjayen mutanen Akwa Ibom.

Umoren ya soki kwarin gwiwar da Akpabio ke da shi na kwace jagorancin siyasar jihar Akwa Ibom a 2027, yana mai cewa cika baki ne kawai yana mai cewa ya yi hakan a 2019.

Kungiyar ta zargi Akpabio da amfani da kalamai na kiyayya da yada kazafi don raba kan garuruwa, masu sarautar gargajiya, shugabannin addini da kungiyoyin matasa.

Sun yi imanin cewa yana kokarin tada zaune tsaye ne da kawo cikas ga gwamnati mai ci a yanzu a jihar saboda wata bukata ta kansa. Kungiyar ta ce tana kyautata zaton ba zai yi nasara ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164