Tinkwal Uwar Daka: ’Yan Najeriya Na Girban Abin da Suka Shuka a 2023, Inji Ministan Buhari
- Tsohon ministan sufuri a gwamnan Buhari, Rotimi Amaechi ya ce ‘yan Najeriya sun cancanci girbar sakamakon duk abin da suka shuka a zaben 2023
- A cewarsa, bai kamata ‘yan kasar su ke kuka da yanayin da ake ciki ba saboda su suka zabar ma kansu shugabannin da suke so
- Ya bayyana hakan ne a yayin da yake martani ga dalilin da yasa ‘yan Najeriya ke yin hijira zuwa kasashen yammacin duniya don neman saukin rayuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
FCT, Abuja – Tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi ya bayyana cewa, ya dace ‘yan Najeriya su girbi abin da suka shuka a zaben da suka yi a wannan gwamnatin.
A cewarsa, ‘yan Najeriya dole su dandana ko ma me ke faruwa saboda su ke da damar zaben shugabannin da suka dace a tsarin dimokradiyya.
Tsohon ministan na Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da gidan talabijin na Arise.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Amaechi, gwamnati ce kadai za ta iya magance matsalolin tattalin arziki, rashin tsari da rashin ayyukan yi.
Tushen matsalolin da ke jawo hijira
Ya kuma yi ishara da cewa, wadannan matsaloli ne ummul haba’isin duk wata hijira da ‘yan kasar ke yi zuwa kasashen waje.
A kalamansa:
“Ina kokarin gudun inda kake son zuwa. Ba za ka yi magana kan lamarin Najeriya ba ba tare da kawo siyasa ba. Domin dole ne a yi magana kan tattalin arziki.
“Wa ke kula da tattalin arziki? Gwamnati ce. Dole ka yi magana kan tsaro da aminci, wa ke kula da lamuran aminci da tsaro? Gwamnati ce.
“Dole ka yi magana kan samar da damammaki, kirkirar ayyuka da sauransu. Don haka, kawai abin da za a ce ‘yan Najeriya suna girban abin da suka shuka. ‘Yan Najeriya na ganin abin da ya cancance shi. Bai kamata ku yi korafi ba.
“A kowanne lokaci ‘yan Najeriya da na damar yin zabe, duk abin da kuka zaba shi kuka cancanta, amma duk da haka, kada mu tabo batun siyasa.”
'Yan adawa sun gamu don tumbuke Tinubu
A gefe guda, masanin siyasa a Najeriya, Farfesa Pat Utomi a wata hira da gidan talabijin na Channels ya bayyana cewa ‘yan takarar shugaban kasa a zaben 2023 sun yanke shawarar kafa jam’iyyar hadaka don fitowa da karfi a gaba.
Da yake karin haske a tattaunawa, ya tattauna kan bukatar kafa sabuwar jam’iyyar siyasa a Najeriya, inda ya jaddada cewa jam’iyyun da ake da su ba su yiwa jama’a hidima yadda ya kamata ba.
Asali: Legit.ng