2027: Babban Jigon PDP Ya Hango Matsalar Dake Tattare da Yin Maja a Kokarin Raba Tinubu da Kujerarsa

2027: Babban Jigon PDP Ya Hango Matsalar Dake Tattare da Yin Maja a Kokarin Raba Tinubu da Kujerarsa

  • Hon. Segun Showunmi ya bugi kirjin cewa jam'iyyar PDP za ta iya lallasa Shugaban kasa Bola Tinubu da jam'iyyarsa ba tare da maja ba
  • Jigon na PDP ya bayyana cewa tsarin hadaka da jam'iyya mai mulki ta yi amfani da shi a 2015 ba lallai ne ya yi wa yan adawa aiki ba a 2027
  • Tsohon dan takarar gwamnan a jihar Ogun ya ce PDP na bukatar sauya jam'iyyar ne kawai, kuma za ta kayar da jam'iyya mai mulki hankali kwance

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Tsohon dan takarar gwamna a jihar Ogun kuma jigon jam'iyyar PDP, Hon. Segun Showunmi, ya bayyana dalilan da suka jam'iyyar hadin gwiwa ba za ta yi tasiri a kan APC ba a 2027.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Jigon PDP ya bayyana dalili 1 da ya sanya hadaka ba ta za ta aiki a kan APC ba

A wata hira da jaridar Punch ta wallafa a ranar Juma'a, 19 ga watan Janairu, jigon na PDP ya bayyana cewa dabarar da APC ta yi amfani da shi wajen tsige PDP a 2015 ba lallai ne ya yi aiki ga yan adawa a 2027 ba.

Jigon PDP ya magantu kan batun maja a 2027
2027: Dalilin da Yasa Maja Ba Zai Yi Tasiri Kan APC Ba, Babban Jigon PDP Ya Yi Bayani Hoto: Segun Showunmi/Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Sun zata za su iya yin amfani da abun da makiyansu suka yi amfani da shi wajen lallasa su a kansu suma.
"Lokacin da makiyansu suka so lallasa su, kimiyya ta nuna cewa maja zai yi aiki da kyau kuma an yi hakan ne tare da jam'iyyar ACN ta Shugaba Tinubu da CPC ta Buhari.
"Haka kuma wasu yan PDP sun bar jam'iyyar don shiga wannan maja, suna masu illata kansu saboda da yawansu sun dawo jam'iyyar yanzu."

"Masu tunanin wannan tsarin malalata ne" - Segun Showunmi

Kara karanta wannan

"Kofar NNPP a bude take ga masu son yin maja", Kwankwaso

Jigon na PDP ya bayyana tsarin maza a matsayin lalaci maimakon tunanin mafita da zai yi tasiri wajen tsige APC.

Hon Showunmi ya bayyana cewa jam’iyyun siyasar da ake sa ran za su yi wannan hadaka duk suna da ‘yan takara wadanda su ma ke son zama shugaban kasa, kuma zai yi wuya a yi magana da su ba tare da aniyarsu ba.

Ya ce:

"Za su shafe shekaru 20 masu zuwa suna fafutuka da kuma yakar kansu kan wanene zai zama shugaban kasa domin dukkansu suna son zama shugaban kasa a lokaci guda."

Jigon na PDP wanda ya tabbatar da sha'awarsa kan kujerar shugabancin jam'iyyar ya bayyana cewa dole ne su hadu wuri guda, su warware sabanin da ke tsakaninsu, su gyara jam’iyyar a ciki domin su samu damar lallasa APC ba tare da maja da kowace jam'iyyar siyasa ba.

Jigon PDP ya ziyarci Buhari

A baya mun ji cewa tsohon mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, Segun Sowunmi, ya bayyana dalilin ziyartar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Showunmi ya bayyana cewa ziyarar da ya kai wa tsohon shugaban ƙasan a kwanakin baya, ya kai ta ne domin tattaunawa kan makomar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng