Kano: Bayan Nasara a Kotun Koli, NNPP Ta Bayyana Matsayin Kwankwaso da Abba Kabir, Ta Fadi Dalilai
- Yayin da ake ci gaba da murnar nasarar Gwamna Abba Kabir a jihar Kano, jam’iyyar NNPP ta fitar da sabuwar sanarwa
- Jam’iyyar ta bukaci hukumar zabe ta INEC ta sabunta sunayen kwamitin shugabannin jam’iyyar
- Ta ce korar manyan 'yan jam’iyyar kamar su Rabiu Kwankwaso da Kawu Abbah na nan daram
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano – Jam’iyyar NNPP a bukaci hukumar zabe ta INEC ta sabunta sunayen kwamitin shugabannin jam’iyyar.
Jam’iyyar ta sanar da haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Asabar 20 ga watan Janairu.
Mene jam'iyyar ke cewa kan Kwankwaso?
Temitope Aluko, shugaban kwamitin amintattun jam’iyyar ya bukaci kafofin sadarwa da su mutunta kundin tsarin jam’iyyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aluko ya ce manyan jam’iyyar kamar su Rabiu Musa Kwankwaso da shugaban kwamitin gudanarwa, Kawu Abbah duk an kore su, cewar Vanguard.
Ya ce an sanar da hukumar zabe mai zaman kanta INEC kan wannan mataki inda ya ce ba su da wani karfin iko a cikin lamarin jam’iyyar.
Mene NNPP ta ce kan Abba Kabir?
Ya ce:
“Kwankwaso da sauran shugabannin kwamitin gudanarwa da Kawu Abbah ke jagoranta duk an kore su, kuma an sanar da INEC.
“Saboda gudun matsala, sabbin shugabannin NNPP, sune Dakta Gilbert Agbo Major a matsayin shugaba sai sakatare, Kwamred Ogini.
“Sannan shugaban kwamitin amintattu shi ne Dakta TKO Aluko, wadannan su ne za su jagoranci jam’iyyar.”
Aluko ya kara da cewa Dakta Aniebonam Boniface shi ne ya kirkiri jam’iyyar wanda ya kasance uban jam’iyya
Sai kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano shi ne shugaban jam’iyyar a jihar Kano, Legit ta tattaro.
Ganduje ya yi ganawa da ‘yan APC a Kano
A wani labarin, shugaban jam’iyyar APC a Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya yi wata ganawa ta musamman da jiga-jigan jam’iyyar a Kano.
Ganduje ya kira ganawar ce don sake duba hukuncin da Kotun Koli ta yanke da kuma daukar matakai don tunkarar gaba.
Manyan jiga-jigan jam’iyyar da ke jihar duk sun halarci zaman inda aka yabi Shugaba Tinubu kan kokarinsa a jam’iyyar.
Asali: Legit.ng