Jam'iyyar PDP Ta Yi Wani Abun Ban Mamaki Bayan Rashin Nasara a Kotun Koli

Jam'iyyar PDP Ta Yi Wani Abun Ban Mamaki Bayan Rashin Nasara a Kotun Koli

  • Jam'iyyar PDP reshen jihar Ogun ta aike da saƙon ta ya murna ga Gwamna Dapo Abiodun kan nasarar da ya samu a Kotun Ƙoli
  • Saƙon ta ya murnar dai na zuwa ne bayan Kotun Ƙolin ta tabbatar da shi a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar
  • Jam'iyyar ta bayyana cewa ta amince da hukuncin da Kotun Ƙolin ta yanke kan shari'ar zaɓen gwamnan jihar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ogun - Jam’iyyar PDP reshen jihar Ogun a daren Juma’a ta taya Gwamna Dapo Abiodun murnar lashe zaɓen gwamnan jihar kamar yadda Kotun Ƙoli ta tabbatar a ranar Juma’a.

Jam’iyyar a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta, Akinloye Bankole ya fitar, ta ce ta amince da gaskiyar hukuncin da kotun ta yanke wanda ya tabbatar da zaɓen Gwamna Dapo Abiodun na jam’iyyar APC, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya bayyana muhimmin abu 1 da ya kamata dan takarar PDP ya yi bayan hukuncin Kotun Koli

PDP ta taya Abiodun murna
Jam'iyyar PDP ta taya Gwamna Abiodun murna Hoto: Prince Dapo Abiodun, Ladi Adebutu
Asali: Facebook

Wani kwamitin alƙalai biyar na kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari’a John Okoro ya yanke hukuncin bai ɗaya, inda ya yi watsi da ƙarar da Oladipupo Adebutu ɗan takarar jam’iyyar PDP a zaɓen gwamnan jihar da ya gabata ya shigar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me jam'iyyar ta ce kan nasarar Gwamna Abiodun?

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"A bisa hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke kan zaɓen gwamna na 2023 a jihar Ogun, ya bayyana cewa lamarin ya kai ga matakin da kundin tsarin mulki ya tanada na ƙarshe kuma magana ta ƙare.
"Kotun Ƙoli ta tabbatar da cewa masu shigar da ƙara sun kasa sauke nauyi na shari’a na tabbatar da cewa zaɓen da aka yi wa Prince Dapo Abiodun a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Ogun baya da inganci.
"Kotun Ƙolin ta tabbatar da cewa ɗan takararmu da jam’iyyar ba su tabbatar da cewa Gwamna Dapo Abiodun bai samu mafi yawan ƙuri’u na halal ba.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta raba gardama, ta faɗi asalin wanda ya lashen zaɓen gwamna a jihar arewa

"A bisa haka, jam'iyyar PDP reshen jihar Ogun na miƙa saƙon taya murna ga gwamnan jihar, Prince Dapo Abiodun da kuma mutanen jihar Ogun."

Jam’iyyar ta kuma bukaci ƴaƴanta da kada su karaya saboda shan kaye da suka sha a Kotun Ƙoli, sai dai su ci gaba da ba da gudummawarsu don ci gaban jihar.

Showunmi Ya Shawarci PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Ogun, Segun Showunmi, ya shawarci jam'iyyar PDP da kada ta yi haɗaka da sauran jam'iyyun adawa.

Showunmi ya yi nuno da cewa jam'iyyar ba ta buƙatar yin haɗaka kafin ta kayar da APC a zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng