Bayan Nasara a Kotun Koli, Gwamnan APC Ya Aike da Sako Mai Zafi Ga Dan Takarar PDP
- Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce ya shaida wa ɗan takarar jam’iyyar PDP, David Ombugadu cewa ba lokacinsa ba ne ya zama gwamna
- Gwamna Sule ya bayyana cewa kafin zuwa Kotun Ƙoli ya gaya wa Ombugadu ya jira lokacinsa ya zama gwamnan jihar Nasarawa
- Ya bayyana hakan ne bayan da Kotun Ƙolin ta tabbatar da hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke wanda ya soke korarsa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana abin da yake faɗa wa ɗan takarar jam’iyyar PDP, David Ombugadu kafin hukuncin Kotun Ƙoli.
Sule ya ce ya sha gaya wa Ombugadu cewa ya jira lokacinsa domin wannan ba lokacinsa ba ne ya zama gwamnan jihar Nasarawa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da gidan Talabijin na Channels tv, a ranar Juma'a bayan da Kotun Ƙoli ta amince da hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke wanda ta soke korar da aka yi masa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kalamansa:
"Na sha fada masa a baya cewa wannan ba lokacinka bane ɗan uwana, ka jira lokacinka."
Gwamna Sule ya aike da saƙo ga masu zanga-zanga
A baya mun kawo rahoto cewa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya aike da saƙo mai zafi bayan zanga-zannga ta ɓarke a jihar kan tabbatar da nasararsa da Kotun Ƙoli ta yi, a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar.
Gwamna Sule ya ce yan jihar su sani cewa, duk irin zanga-zangar da zasu yi ba za ta sauya komai daga hukuncin da Kotun Kolin ta yanke ba, cewa gwanda su rungumi zaman lafiya domin shi ne mafita gare su.
Kotun Ƙoli Ta Tabbatar da Nasarar Gwamna Sule
A wani labarin kuma, kun ji cewa Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule na jam'iyyar APC a matsayin halastaccen gwamnan jihar.
Kotun mai alƙalai biyar ta yi watsi da ɗauƙaƙa ƙarar da ɗan takarar jam'iyyar PDP, David Ombugadu, ya kai gabanta yana ƙalubalantar hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke.
Asali: Legit.ng