Cikin Gwamnan APC Ya Duri Ruwa Bayan Jam’iyyar Ta Magantu Kan Ba Shi Tikiti, Ta Fadi Dalili

Cikin Gwamnan APC Ya Duri Ruwa Bayan Jam’iyyar Ta Magantu Kan Ba Shi Tikiti, Ta Fadi Dalili

  • Da alamu Gwamna Lucky Aiyedatiwa zai sha bakar wahala kafin ya samu tikitin tsayawa takarar gwamna a jihar
  • Jam’iyyar APC mai mulki ta bayyana cewa ba za ta bai wa Gwamna Lucky Aiyedatiwa tikiti babu hamayya ba
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata hira da Kakakin jam’iyyar na kasa, Felix Morka ya yi da ‘yan jaridu a A uja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo – Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta bayyana cewa ba za ta bai wa Gwamna Lucky Aiyedatiwa tikiti babu hamayya ba.

Wannan na zuwa ne yayin da ake shirin gudanar da zaben jihar a ranar 16 ga watan Nuwambar wannan shekara, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Kano: Kwankwaso Ya faɗi makircin da aka Shirya ƙulla masa idan Gawuna ya yi nasara a Kotun Koli

Jam'iyyar APC ta magantu kan bai wa Lucky tikitin takara a zabe
Jam'iyyar APC ta bayyana matsayarta kan tikitin Gwamna Lucky na Ondo. Hoto: Lucky Aiyedatiwa.
Asali: Facebook

Mene APC ke cewa kan tikitin Ondo?

Gwamna Lucky na jihar Ondo ya dare kujerar mulki ne bayan mutuwar Rotimi Akeredolu a watan Disambar 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam’iyyar ta ce har zuwa yanzu ba ta yanke shawara ba ko za ta tura tikitin wani yanki na jihar ko sabanin haka.

Kakakin jam’iyyar na kasa, Felix Morka shi ya bayyana haka yayin hira da gidan talabijin na Channels.

Morka ya ce jam’iyyar APC ta na bin tsarin dimukradiyya inda take ba da dama ga kowa don neman kujerar siyasa.

Yadda tsarin jam'iyyar APC ya ke

A cewarsa:

“Ba mu yi wata tattaunawa kan wannan ba, amma mu jam’iyyar dimukradiyya ce da ci gaba.
“Ba za mu bai wa mutane haka kawai ba, dole su za su tabbatar wa kansu su kuma nema da kansu.

Kara karanta wannan

Ganduje ya bayyana jiha 1 tal da jam'iyyar APC za ta kwato daga hannun PDP a 2024

“Dole dukkan masu takara su shiga zaben fidda gwani, a APC ba mu ba da abu haka a banza, kowa zai shiga a dama da shi.”

Kan maganar tikitin zaben gwamnan jihar Ondo, Morka ya ce har yanzu ba su yanke shawara kan tikitin ba.

Ya kara da cewa:

“Har yanzu ba mu yanke shawara ko zamu tura tikitin wani yanki ba ko sabanin haka, za mu fada idan mun gama tataunawa.”

Shugaban APC ya yi murabus a Edo

Kun ji cewa, shugaban Jam’iyyar APC a jihar Edo, David Imuse ya yi murabus ana daf da gudanar da zaben gwamna a jihar.

Shugaban ya ce ya yi murabus din ne a karan kansa inda ya ce ya na sha’awar tsayawa takarar gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.